Jam’aa sun yi wa wani lakcara kuma fasto duka tare da neman yi masa tsirara kan zargin satar mazakuta a yankin Wurukum da ke garin Makurdi a Jihar Binuwai.
Dokta Emmanuel Aime, wanda malami ne a Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Akawe Torkula da ke jihar, ya je yin wa’azi ne a safiyar laraba a kusa wa wani banki inda wani ya yi kururuwa cewa an sace masa mazakuta.
Mutanen da suka ritsa shi, sun bayyana cewa fitowar Dokta Emmanuel daga cikin banki ke da wuya wani matashi ya yi ihu da zargin shi da sace masa mazakuta.
Nan take mutane suka far masa da duka suka yi masa jina-jina suka yayyaga kayansa, saura ɗan kamfai kafin sojoji da wasu jami’an tsaro suka yi suka kwace shi.
KU KUMA KARANTA: An yi wa ‘yan sanda biyar duka a Abuja, a ƙoƙarin ceton wanda ake zargi da satar mazakuta
Wani shaida a wurin ya ce daga baya an binciki matashin da ya yi zargin an sace masa mazakuta, amma aka same shi lafiya, shi ne aka garzaya da shi ofishin ’yan sanda.
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP. Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin, wanda ta bayyana takaicinta a kansa