An kwantar da ɗaliban firamare 18 a asibiti bayan cin abincin makaranta

0
160

An kwantar da ɗaliban wata makarantar firamare su 18 a asibiti bayan da suka ci abincin da Gwamantin Jihar Osun take ciyar da ɗalibai a makarantu.

Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Kolapo Alimi ya ce gwamnan jihar, Ademola Adeleke ya ba da umarnin gudanar da bincike a kawo masa rahoto kan abin da ya faru.

Baya ya bayyana cewa daga baya an sallami yaran daga asibitin bayan da sun samu sauki.

Alimi ya ce Gwamna Adeleke ya ba da umarnin dakatar da shirin ciyar da ɗalibai a makarantar da abin ya faru.

KU KUMA KARANTA: Cutar Kyandar Biri; Masanin Kimiya Ya Fara Wayar Da Kan Dalibai Bisa Rigakafin Kamuwa Da Cututtuka

Wannan abu dai ya faru ne a makarantar St. James B, Owo-Ope da ke Osogbo, babban birnin jihar.

Kwamishinan ilimin ya ce an gayyaci mai girkin abinci a makarantar zuwa gidan gwamnati, inda aka ba da umarnin tabbtar da ingancin abicin da ake ba wa ɗalibai.

Gwamnatin jihar ta kuma ziyarci iyayen ɗaliban tare da biyan kuɗin asibitinsu na jinyar.

Leave a Reply