An kori ‘yan sanda biyu daga aiki bayan samun su da yin fashi da makami

0
136

An kori Sufeto ‘yan sanda biyu Sunday Adetoye da Ogunleye Stephen da ke aiki a hedkwatar rundunar ‘yan sanda ta Zone 2, Onikan, Legas, bisa laifukan da shiyyar ta bayyana a matsayin fashi da makami, cin hanci da rashawa da kuma gudanar da ayyukansu ba bisa ka’ida ba.

Mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sanda, mai kula da shiyya ta 2, AIG Mohammed Ali, ne ya bayar da umarnin korar nasu bayan yin wani cikakken bincike.

Rahotanni sun bayyana cewa Sufeto Adetoye mai lamba 279495 da Stephen mai lamba 223521 tare da wasu ‘yan ƙungiyar Vigilante guda biyu Semiu Afisu da Abidoye Femi, da wani direba mai suna Charles John, sun kai farmaki wani gida a unguwar Obada-Oko a jihar Ogun da misalin karfe 1 na safe 10 na dare, Nuwamba 23,2023.

An ce an kama su da bindigogin Submachine SMG guda biyu da kuma harsasai.

KU KUMA KARANTA: An kama mutane huɗu da ake zargi da fashin banki a Benuwe, wanda ya yi sanadin mutuwar DPO da ‘yan sanda uku

Rahotanni sun ce sun binciki gidan wani Taiwo Monsuru da Akintola Sunday, ba tare da izini ba, inda suka yi awon gaba da wayoyin iPhone guda biyar, wayar Samsung daya, wayar Tecno daya da kwamfutocin tafi da gidanka guda biyu.

Da yake bayyana yadda aka kama su, jami’in hulɗa da jama’a na shiyyar, SP Umma Ayuba, ya ce “Jami’an ‘yan sandan da ke yankin Ifo ne suka tare hanya bayan da wasu mazauna gidan suka sanar da su lamarin, tare da bayanin motar.

Hakan ya kai ga damƙe mutanen da ke cikin motar, ba tare da ASP Ajayi Victor da ya jagoranci aikin ba.

Leave a Reply