No menu items!

Sample Page Title

Date:

An kori wata malamar jinyar masu lalurar ƙwaƙwalwa a yankin Shropshire da ke Birtaniya bayan ta yi lalata da wani majinyaci.

Matar, mai suna Samantha Bourton wadda ke aiki da gidauniyar ma’aikatar lafiya ta Birtaniya, an gano cewa tana zuwa gidan majinyacin har a lokutan da ba na aiki ba.

Wani kwamitin bincike da aka kafa ya kuma gano cewa ta ƙi bayar da rahoton cewa marar lafiyan ya taɓa yin tunanin kashe kansa.

Hukumar tantance malaman jinya da ungozoma ta Birtaniya ta ce ba za a lamunci wannan ɗabi’a ta malamar jinyar ba.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta yanke wa mai fenti hukuncin ɗaurin rai da rai bisa laifin lalata ’yar maƙwabciyarsa

Ganin cewa ƙimar aikin zai zube idan aka bar ta ta ci gaba da aiki.

A cikin wani bayani, kwamitin ya ce Misis Bourton ba ta musanta cewa ta sadu da majinyacin ba a watan Mayu na 2021.

Kwamitin ya ce ta tuntuɓi mutumin ta hanyar amfani da lambar waya ta ƙashin kanta sannan ta ziyarce shi sau biyu a lokutan da ba na aiki ba.

Sai dai an gano cewa sauran ziyarar da ta kai masa daga baya, ba ta yi ne domin yin lalata da shi ba.

A yanzu an dakatar da ita na wata 18, a matsayin matakin farko, inda za ta iya ɗaukaka ƙara a tsakanin wa’adin.

Sai dai idan ba ta ɗaukaka ƙara ba, korar ta tabbata.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

2 COMMENTS

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...