An kori ɗan sandan da ya yi wa yarinyar da ke tsare a ofishin ‘yan sanda fyaɗe

0
228

Rundunar ‘yan sandan jihar Benuwe ta kori ɗan sanda mai suna Belasa Iyangedue, bisa zargin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 16 fyaɗe, mai suna Nguemo Terkaa, yayin da take tsare.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bartholomew Onyeka ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Talata, 3 ga watan Oktoba a Makurɗi.

CP Onyeka ya ce ɗan sandan da aka kora ya aikata laifin a ofishin ‘yan sanda na Tse Agbaragba, da ke ƙaramar hukumar Konshisha.  Ya ƙara da cewa jami’in da aka kora tuni ya fuskanci tuhuma.

Tum farko a ranar 15 ga watan Agusta aka tsare yarinyar saboda laifin ɓata wa wani suna.

A yayin da take tsare, an zargi ɗan sandan ya ɗauke ta daga ɗakin da take ciki da daddare, inda ya shigar da ita ɗaya daga cikin ofis tare da yi mata fyaɗe.

KU KUMA KARANTA: Wani Dattijo ya yi wa yarinya kurma fyaɗe ta mutu

Washegari bayan an bayar da belin wadda aka yi wa fyaɗen, ta kai rahoto ga DPO, inda aka kama ɗan sandan kuma aka shigar da ƙarar zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar a Makurɗi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Bartholomew Onyeka, ya ce, “Dan sandan da aka kora ya aikata laifin a ofishin ‘yan sanda na Tse Agbaragba, ƙaramar hukumar Konshisha.

“’Yan sanda hukuma ce mai ɗa’a kuma kasancewarta hukuma ce da ke da alhakin daƙile aikata laifuka da yaƙi da laifuka, ba a yarda irin waɗannan mutane su zauna a cikin tsarin ba.

“Ba kawai an kore shi ba, yana fuskantar tuhuma.”

Wannan zargin fyaɗen ya zo ne ƙasa da shekara guda bayan da abokansa suka yi bikin Belasa Iyangedue a dandalin sada zumunta na Facebook biyo bayan faretin kammala samun horon aikin ɗan sanda da ya yi bayan ya kwashe watanni yana samun horon aikin ‘yan sanda.

Leave a Reply