An kashe ‘yan bindiga da ɓarayin daji 9,800 cikin shekara 1 – Ministan tsaro

0
89

An kashe ‘yan bindiga da ɓarayin daji 9,800 cikin shekara 1 – Ministan tsaro

Ministan tsaron Najeriya, kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar a hirarsa ta musamman da Shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, Aliyu Mustapha, ya tabo batuttuwa da dama game da tsaro musamman a arewancin Najeriya.

Badaru ya ce tun ya fara aiki, ya gana da dukkan manyan tsoffin sojoji da ma’aikatan tsaro, ciki har da tsohon Shugaban mulkin sojin Najeriya, Abdulsalam Abubakar, don samun shawarwarin magance matsalar tsaro.

Albarusai da makaman da aka samu a motar waɗannan ‘yan bindiga bayan da aka kashe tara daga cikinsu, aka kama guda biyu
Albarusai da makaman da aka samu a motar waɗannan ‘yan bindiga bayan da aka kashe tara daga cikinsu, aka kama guda biyu
Ya kuma nanata cewa babban matsalar tsaro shi ne rashin haɗin kan shuwagabannin tsaro, amma ya zuwa yanzu, an samu haɗin kai a tsakanin shuwagabannin na tsaro da suka hadda da ‘yan sanda da jami’an fararen hula wanda shi ne tushen nasarorin da ake ta samu.

KU KUMA KARANTA:Gwamnan Zamfara ya jinjinawa jami’an tsaro tare da yin jaje ga wanda iftila’in ya shafa

Ya ƙara da cewa cikin shekara ɗayan da aka cika, an samu nasarar kashe ‘yan ta’adda da ɓarayin daji kusan 9,800, an kuma kama kimanin ‘yan bindiga 7,000, sannan kuma an ƙwato mutanen da aka sace kusan 4,700.

Badaru ya ce babban matsalar da su ke fuskanta shi ne na samun haɗin kan jama’a wajen ba da ingantaccen bayanai.

Leave a Reply