An kashe sojojin Najeriya a harin kwanton-ɓauna a jihar Neja

0
164

Rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya ta ce wasu ƴan bindiga sun kashe sojojinta shida a wani harin kwanton-ɓauna da suka kai musu a jihar Neja da ke tsakiyar ƙasar.

Mai magana da yawun rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, wanda ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ranar Lahadi da maraice, ya ƙara da cewa su ma sojojin Najeriya sun kashe ƴan bindiga da dama yayin fafatawar.

A cewarsa, ƴan ta’addan sun yi kwanton-ɓauna ga dakarunsu da aka tura wasu yankunan ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja ranar 19 ga watan Afrilun 2024, inda suka gwabza faɗa “sannan suka kawar da ƴan ta’adda da dama tare da karɓe wasu daga cikin makamansu”.

“Abin baƙin ciki shi ne, dakarun sun fuskanci ƙalubale domin kuwa 6 sun mutu, cikinsu biyu manyan sojoji ne, yayin da huɗu kuma ƙananan sojoji ne,” in ji Manjo Janar Nwachukwu.

KU KUMA KARANTA: Babban Hafsan Sojojin Kenya, Francis Ogollaya, ya mutu a hatsarin helikwafta

Ya ƙara da cewa tuni aka sanar da iyalan sojojin da suka mutu, sannan aka yi wa Musulmai daga cikinsu jana’iza a maƙabartar sojoji da ke birnin Minna.

Rundunar sojojin ta Najeriya ta ce dakarunta suna can suna farautar sauran ƴan ta’addan da suka tsere da zummar cim masu, kuma ta yi kira ga mazauna yankin da lamarin ya faru su ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba.

Leave a Reply