An kashe mutane biyu, an raunata ɗan Sanda a rikicin ƙabilanci a Ebonyi

0
434

Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi ta tabbatar da cewa an harbe mutum biyu har Lahira tare da jikkata wani jami’in ‘yan sanda a lokacin da mayaƙan Ishinkwo suka far wa jama’a a kan hanyarsu ta dawowa aiki a hanyar Abaomege/Ishinkwo a ƙaramar hukumar Onicha.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Onome Onovwakpoyeya ya sanyawa hannu, ta ce harin ya biyo bayan wani sabon rikicin ƙabilanci da ya ɓarke tsakanin al’ummomin biyu kan taƙaddamar filaye da aka daɗe ana yi.

Ta yi iƙirarin cewa “Oshinkwo Warriors” sun harbe mutane uku ciki har da ɗan sanda da ke dawowa gida bayan aiki a yankin Abaomege-Oshinkwo rikicin ƙabilanci.

KU KUMA KARANTA: Rikicin Kutep da Fulani, an kashe mutane 8 a Taraba

An garzaya da waɗanda abin ya shafa asibiti. An tabbatar da mutuwar biyu daga cikin waɗanda abin ya shafa amma ɗan sandan yana karɓar magani, in ji kakakin ‘yan sandan.

Ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sunday Falaye ya yi ƙira da a farauto waɗanda ake zargi da guduwa tare da bayar da tabbacin cewa za a kama waɗanda suka aikata laifin tare da fuskantar fushin doka.

Wani mazaunin yankin da ya ɗauki matakin sanar da jama’a a dandalin shi na sada zumunta ya rubuta cewa, “ku guji Abaomege-Ishinkwo axis yau 6/6/2023.

Mutane uku daga Ukawu da mutum ɗaya da ke zama matar kawuna sun mutu da safiyar yau a hanyarsu ta zuwa Abakaliki.”

Wani mazaunin garin da ya zanta da manema labarai bisa dalilin sakaya sunansa ya ce duk da ƙoƙarin da gwamnatin ƙarshe ta Gwamna David Umahi ta yi na kawo ƙarshen rikicin; mutanen Isinkwo ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen kai wa al’ummar Abaomege hari.

Wasu majiyoyi da ba a tabbatar da su ba sun ce an yi asarar rayuka sama da 200 da kadarori na biliyoyin nairori sakamakon rikicin filaye tun shekarar 2020 da rikicin ya fara.

Umahi a ƙoƙarinsa na kawo ƙarshen rikicin ya umarci ma’aikatar filaye ta jihar da ta karɓe filin da ake taƙaddama a kai.

Rikicin da ya sake ɓarkewa ya sa masu ababen hawa ke bin hanyar don bin hanyoyin daban yayin da yawancin mazauna yankunan biyu suka bar gidajensu saboda fargabar ci gaba da kai hare-hare.

Leave a Reply