An kashe ma’aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya 64 a Gaza

0
213

Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijirar Falasɗinawa, (UNRWA) ta bayyana cikin baƙin ciki cewa ma’aikatanta 64 ne suka rasa rayukansu a Gaza a rikicin Isra’ila da Hamas.

Hukumar ta ƙara da cewa wani abin takaicin shi ne, ɗaya daga cikin ma’aikatan da aka kashe harda ɗaukacin iyalinsa da suka haɗa da ‘ya’ya takwas da matarsa ​​yayin da suke gida.

KU KUMA KARANTA: Adadin mutanen da suka rasa muhalli a sassan duniya ya zarta miliyan 114 — MƊD

Mai magana da yawun hukumar, Juliette Touma, ta bayyana damuwa game da cunkoso a matsuguni 450 da suke gudanarwa a faɗin Gaza, inda jimillar mutane 670,000 suka nemi mafaka.

Lamarin dai ya yi ƙamari, inda rahotanni ke cewa cututtuka kamar su zawo da gudawa suna yaɗuwa.

Ana buƙatar tsagaita wuta na jin ƙai cikin gaggawa saboda hatta wuraren da ya kamata a kiyaye, da suka haɗa da majami’u da masallatai da wuraren Majalisar Ɗinkin Duniya, abin ya shafa.

Leave a Reply