An nuna wakilin tashar Aljazeera kai tsaye a talbajin rungume da gawar matarsa da ‘yarsa da kuma ɗansa a abin da tashar ta ce sun mutu ne sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai Gaza.
Wa’el Al’dahdud ya ce iyalansa sun bar arewacin Gaza inda suka koma kudancin yankin domin cika umarnin da Isra’ila ta ba su na ficewa daga yankin.
Abokin aikinsa Hoda Abdel-Hamid ya bayyana shi a matayin ɗan jarida mai bayar da bayyanai kan gwagwarmayar Falasɗinawa a Gaza.
Kawo yanzu da rundunar soji Isra’ila ba ta ce komai ba game da kisan iyalan ɗan jaridan.
Tun da farko, jami’an lafiya a Gaza sun ce fiye da Falasɗinawa 750, ciki har da ƙananan yara 344 ne suka mutu cikin kwana guda, sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza.