No menu items!

Sample Page Title

Date:

Aƙalla Falasɗinawa 100 aka kashe a wasu hare-hare da aka kai cikin dare da safiyar Laraba a Gaza, a yayin da rundunar sojin Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare yankin da ta yi wa ƙawanya gabanin cimma yarjejeniyar da za ta fara aiki a ranar Alhamis.

Dukkan ɓangarorin sun tabbatar da wata yarjejeniya da aka cimma tsakanin Hamas da Isra’ila, da sa hannun Washington da Qatar, wadda ta taimaka wajen cimma yarjejeniyar da za ta sa a tsagaita wuta na wucin gadi a mummunan yaƙin da ya shiga mako na bakwai.

A cikin yarjejeniyar, a cikin kwana huɗu Hamas za ta saki aƙalla mutum 50 daga cikin 240 da take garkuwa da su tun lokacin da ta kai hari Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoba, inda ita ma Isra’ila za ta saki Falasɗinawa fursunoni da take tsare da su.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...