An kashe ɗalibi da duka a makarantar Al-Azhar Academy da ke Zariya

0
233

A ranar Juma’a ne muka samu labarin wani mummunar hukunci da hukumar makarantar Al-Azhar Academy da ke bayan Ƙofar Gayan Zariya suka yi wa wani ɗalibinsu mai suna Marwanu Nuhu Sambo, ɗan JS3 (Basic 9), wanda a yayin wannan hukuncin sai da suka aika shi har lahira, saboda tsananin hukunci.

Bayan kisan wannan yaro da suka yi, ba su sanar da iyayensa ba har sai da iyayen yaron suka riƙa jin raɗe-raɗin cewa an kai yaron asibitin Al-Ridha Clinic, inda suka garzaya can domin tabbatar da labarin da suke samu game da ɗan nasu, amma bayan sun samu likitan, sai ya faɗa masu cewa, shi ba mara lafiya aka kawo masa ba, gawa ce aka kawo masa.

Wakilin jaridar Daily Trust ya bayyana cewa, ya kai ziyara har wannan makaranta domin tabbatar da wannan labarin, a inda ya zanta da wasu ɗalibai 2 da kuma wani yaro mai sayar da abinci a makarantar, tare da wata mata duka suka tabbatar masa da faruwar wannan al’amari.

KU KUMA KARANTA: Ɗalibin jami’a ya rasu yana tsaka da rubuta jarrabawar ƙarshe a jami’ar Gombe

Daga nan, na garzaya zuwa gidan da ɗalibin da aka kashe yake, na tattauna da wasu iyayensa guda biyu, duka suka tabbatar masa da faruwar abin, har suka kai ni inda ake yi wa gawar yaron wanka. Inji shi.

Bayan nan, ya sake zuwa wurin wasu ɗaliban makarantar, inda ya zanta da su, ɗaya daga cikin yaran ajinsu ɗalibin da aka kashe.

Sannan ya labarta masa yadda malaman suka aikata wannan hukunci.

Yaron ya ce, mataimakin shugaban makarantar (vice principal) shi ya zo da yaron gaban assembly, inda suka riƙa yi masa bulala babu ƙaƙƙautawa tare da shugaban makarantar (Principal), tun suna iya ƙirga bulalar har suka ɓata a lissafi, inda yaron ya tabbatar masa da kansa ya ƙirga bulala aƙalla 105 wanda aka yi wa yaron a gaban assembly, daga nan kuma suka wuce da shi office, suka cire masa riga, suka bar shi da gajeren wando kawai, suka ci gaba da dukan sa har yaron ya yi yunƙurin gudu, amma aka sa (prefects) na makarantar suka riƙe shi suka koma da shi, suka ci gaba da dukan sa har sai da suka cire masa haƙora, suka kashe shi.

Duk kuma dalilin wannan hukuncin kawai, shi ne ba ya zuwa makaranta kullum.

Bayan sun kashe yaron, suka fito da shi waje, suka aje shi a hanyar bayi har aka tashi makaranta.

Abin da zai ƙara ba ku mamaki shi ne, har zuwa karfe 8:30 na daren nan da kuma lokacin da nake wannan rubutun, babu wasu hukuma na wannan makaranta da suka halarci gidan wannan iyayen yaron.

Muna ƙira ga hukuma, da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, da hukumar ilmi ta jihar Kaduna da su shiga cikin wannan lamari, domin nema wa wannan ɗalibi haƙƙinsa, tare da hukunta wannan makaranta daidai da laifin da ta aikata, domin mun daɗe muna samun labarin irin mummunar hukuncin da ake yi a wannan makaranta mai suna Al-Azhar, wadda take ƙofar Gayan Zariya, sumar da yara ɗalibai ya zama ruwan dare a wannan makaranta saboda tsananin hukunci.

Leave a Reply