An karrama matashin da ya tsinci dala 10,000 a Kano
Hukumar Karɓar Koke-Koke da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano ta karrama Awwal Dankode, ma’aikacin filin jirgin saman Malam Aminu Kano, da lambar yabo bayan ya dawo da dala 10,000 da ya tsinta a cikin jirgin sama.
Dankode, tare da wasu mutum bakwai, an karrama su a matsayin gwarazan yaƙi da cin hanci a wani taro na musamman da aka gudanar a Kano don murnar Ranar Yaƙi da Cin Hanci ta Duniya.
Dankode ya bayyana cewa lokacin da ya tsinci kuɗin, ya ga dacewar mayar da su, haka ne ya sa ya yanke shawarar mayar da su.
“Lokacin da na tsinci kuɗin, sai na ce yanzu haka wani yana can yana neman su, shi ya sa na yanke shawarar mayar da su.”
Bayan haka, an karrama shi a hedikwatar NAHCON da ke Legas, inda aka ba shi kyautar kuɗi da kuma ƙarin girma.
Daga cikin waɗanda aka karrama akwai Umar Bello, shugaban unguwar kusa da Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, wanda ya taimaka wajen warware rikicin fili da ya ɗauki shekaru 25.
Mai Shari’a Dije Abdu Aboki, alƙalin babbar kotun Jihar Kano, ta samu karramawa saboda canje-canjen da ta kawo a fannin shari’a wanda ya rage cin hanci.
Sauran waɗanda aka karrama sun haɗa da ACP Suleman Gusau, Salisu Balarabe (daraktan shirin Kwana 90), Lauya Rabi Ibrahim Waya, Abba Al-Mustapha, da CSP Sunday Osogwu, saboda kokarinsu a yaƙi da cin hanci.
KU KUMA KARANTA: An karrama ɗan agajin da ya tsinci miliyan 100
Shugaban hukumar, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta sanya hannu kan kafa rijistar bayanan laifuka da kuma ɗaukar alhakin tuhumar masu aikata laifukan sayen fili a jihar.
Ya kuma bayyana cewa hukumar ta gano wata ƙungiya mai aikata cin hanci a harkar sayen fili wacce ake kira ‘Yan Ƙasa ta Allah ce.
Ya ce wannan ƙungiya tana da ƙarfin kuɗi da kuma shafar hukumomi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya sanar da sabbin tsare-tsare da za su ƙarfafa yaƙi da cin hanci a jihar, ciki har da rijistar bayanan laifuka da kuma haɗin gwiwar gwamnati a yaƙi da cin hanci.