An karrama ɗan agajin da ya tsinci miliyan 100

0
164

An bai wa ɗan agajin Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatus Sunnah (JIBWIS), Salihu AbdulHadi Kankia, kyautar kujerar aikin hajji sakamakon dawo da naira miliyan 100 da ya tsinta a Jihar Bauchi.

Wannan na zuwa ne lokacin bikin rufe taron shirin tafsirin watan Ramadan na bana da malaman addinin Musulunci suka yi a Jihar  Bauchi.

Daraktan Ƙungiyar Agaji na ƙasa, Injiniya Mustapha Imam Sitti ne, ya gabatar da Kankia don a yaba masa kan dawo da makudan kudin da ya yi.

A wani sako da JIBWIS reshen Jihar Bauchi ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce, “Kankia ya gano wata jaka dauke da makudan kudade sama da naira miliyan 100.

KU KUMA KARANTA: Yadda aka karrama mai KEKE-NAPEP da ya dawo da miliyan 9 da ya tsinta a babur ɗinsa a Yobe

“Maimakon ya tsere da kuɗin, sai ya garzaya ofishin ‘yan sanda inda ya mika jakar kuɗin, ‘yan sandan sun yi nasarar gano mai jakar, kuma sun tabbatar da babu abin da ya ɓata a ciki.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Ƙungiyar Izala ta karrama shi da lambar yabo tare da biya masa kujerar aikin hajjin bana.

“Bugu da ƙari, dan majalisar dokokin Jihar Zamfara, Hon. Abdulmalik Zannan Bangud, ya ba shi kyautar naira miliyan biyu.

“Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi, ya  ba shi kyautar mota ƙirar bas don fara neman kuɗi da ita.”

Leave a Reply