An kama yaro ɗan shekara 16 a Kebbi bayan ya yi wa ƙananan yara 2 fyaɗe

An kama wani matashi ɗan shekara 16 Habibu Umar bisa zargin yi wa ƙananan yara biyu fyaɗe a unguwar Badariya a Birnin kebbi.

An kama shi ne da sanyin safiyar ranar Talata 21 ga watan Nuwamba, 2023 bayan da ya ruɗe ƙananan yara mata biyu da ke zaune a Badariya zuwa wani daji da ke kusa tsakanin yankin Badariya da barikin sojoji inda ya lalata ‘yan matan biyu masu shekaru 6 da 5 ta hanyar yi masu fyaɗe.

Shafin labarai na yanar gizo isyaku.com  ya tattaro cewa Kwamanda Ahmad Waziri, DC Aminu Abdullahi da Samaila Karo Kwamanda Bayan Kara ne suka gudanar da aikin a karkashin kwamitin tsaro da ke aiki ƙarƙashin Masarautar Gwandu ƙarƙashin jagorancin Alhaji Bello Nahaliku.

Tun da farko dai kwamitin ya gabatar da wanda ake tuhuma da waɗanda aka yi wa fyade a gaban Ubandoma na Gwandu, inda wanda ake zargin ya amince da aikata laifin a fadar bisa raɗin kansa yayin da ake masa tambayoyi.

KU KUMA KARANTA: Mutumin da ake zargi da yi wa ’yar shekara 2 fyaɗe ya ɗora wa barasa alhaki

Binciken lafiya na farko da ma’aikacin lafiya daga Cibiyar Kiwon Lafiya ta Kebbi da ke ofishin Hisbah na fadar Ubandoma suka yi, ya tabbatar da an keta budurcin ƙananan yaran biyu.

Hakazalika, gwajin kwayar cutuka da jami’an kiwon lafiya suka gudanar ya nuna wanda ake zargin yana ɗauke da Hepatitis B, amma yaran basu kamu dacutar ba a sakamakon gwajin farko. Sai dai za a buƙaci ‘yan matan su maimaita gwajin bayan makonni biyu.

Jaridar isyaku.com ya tattaro cewa an miƙa ƙarar ga hedikwatar Hisbah ta jihar Kebbi.  Bayan binciken farko da kwamandojin Hisbah suka yi, an mayar da shari’ar ga rundunar ‘yan sandan Najeriya Area command reshen Birnin kebbi domin bincike da gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kotu.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *