An kama ‘yan sandan Najeriya biyu kan zargin karɓar rashawa daga Baturiya

0
182

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Juma’a ta tabbatar da kama wasu jami’anta biyu masu mukamin kwanstabul kan zargin karɓar rashawa daga wata Baturiya. Lamarin ya faru ne a kan hanyar Iseyin zuwa Ogbomosho da ke Jihar Oyo.

A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga wasu ‘yan sanda biyu sun tsayar da wata Baturiya wadda ta ce ta taho tun daga ƙasar Netherlands a kan babur wadda ta ce za ta je Abuja.

A cikin bidiyon, an ji ‘yan sandan suna tambayar Baturiyar me ta kawo musu bayan haka kuma aka ji suna rokonta kuɗi cikin raha. Sai dai a sanarwar da mai magana da yawun ‘yan sandan Najeriya Muyiwa Adejobi ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa an kama ‘yan sandan ne saboda halayyar da suka nuna ta rashin ƙwarewar aiki.

Adejobi ya kuma tabbatar da cewa tuni kwamishinan ‘yan sandan Najeriya reshen Jihar Oyo Adebola Ayinde Hamzat ya tanadi tsarin ladabtarwa kan lamarin ba tare da ɓata lokaci ba.

KU KUMA KARANTA: Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano ta damƙe magidanci da ɗansa bisa zambar naira biliyan huɗu

“Hukumar ‘yan sanda ta yi Allah-wadai da wannan aika-aika tare da ba da umarnin hukunta ‘yan sandan da kuma shi kansa jami’in ‘yan sandan da ke sa ido a kan su.”

Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar ‘yan sandan ƙasar za ta ci gaba da matsa kaimi wurin gudanar da shirye-shirye na sake wayar da kai da horo ga ‘yan sanda domin guje wa afkuwar irin wannan lamarin.

Ba wannan ne karon farko da rundunar ‘yan sandan Najeriya ke fitar da sanarwar zargin jami’anta da rashin ɗa’a ba.

Ko a kwanakin baya sai da rundunar ‘yan sandan ta yi tir da halayen wasu jami’an nata bayan wani bidiyo ya nuna wasu jami’anta sun bi ta kan wani mutum da mota.

Haka ma a kwanakin baya rundunar ‘yan sandan ta sallami wasu jami’anta uku da ke ba mawakin nan na Najeriya Dauda Kahutu Rarara kariya sakamakon laifukan da suka haɗa da amfani da bindiga ba bisa ƙa’ida ba da wuce gona da iri da rashin ɗa’a

Leave a Reply