An kama ’yan sanda suna gadin dillalin miyagun ƙwayoyi

0
180

An tsare wasu ’yan sanda biyar da aka kama suna rakiya da ba da kariya ga dillalan miyagun ƙwayoyi wajen yin safarar hodar Iblis.

Dubun ’yan sandan da ake tsare a halin yanzu ta cika ne a lokacin da suke rakiyar dilar hodar Iblis mai tarin yawa da misalin ƙarfe 3 na asuba a jihar Legas.

Waɗanda aka kama ɗin suna aiki ne a runduna ta musamman na shugaban ’yan sanda kan yaƙi da muggan laifuka.

An kama su ne bayan musayar wuta da ’yan sandan farin kaya da suka samu labarin mugun aikin, suka kuma yi ƙoƙarin kama dillalan ƙwayoyin a yankin Vicoria Island.

Wani babban dan sanda ya shaida wa wakilinmu cewa bayan an tsayar da waɗanda ake zargin domin bincike sai “suka fara barazana ga jami’anmu suna harbi a iska.

“Amma duk da haka, jami’anmu suka ki janyewa su bar su su wuce, da aka bincika kuma sai aka kama su da tulin miyagun ƙwayoyi,” waɗanda bayanai suka nuna hodar iblis ce.

KU KUMA KARANTA: EFCC ta kama tagwaye ’yan yahoo

Jami’in ya ci gaba da cewa, “ana cikin haka sai jami’an NDLEA suka iso wurin, amma da suka nemi su tafi da ƙwayoyin sai waɗancan suka ci gaba da harbe-harbe, suna neman hana su.

“Hakan ne ya sa sojoji suka iso wurin, suka tafi ƙwayoyin barikinsu da ke Bonny Camp, daga nan kwamandansu ya kira AIG mai kula da Zone 2, aka zo aka tafi da ita.”

Waɗanda aka kaman sun a cewarsa, sun haɗa da wani muƙamin DSP, Fayomi Abraham, ASP Emmanuel Bentong, Inspector Salami Femi, Inspector Ashimi Adedokun da Sajan Alex Akeredolu.

Wani mai mukamin mataimakin Kwamishinan ’yan sanda  Ali Mohammed Ari ne ya kai su ofishin AIG Ali domin fuskanar bincike in ji jami’in.

Wakilinmu ya nemi AIG mai kula da Zone 2, Ali Mohammed Ari, domin ƙarin amma bai amsa ƙiran ba.

Leave a Reply