Sojojin ruwan Najeriya da ke sintiri sun zaƙulo wasu matasa tara da suka ɓoye a farfelar wani jirgin ruwa da nufin zuwa Turai ba bisa ƙa’ida ba.
A ranar Litinin Kwamandan jirgin, Commodore Kolawole Oguntuga, ya sanar cewa an gano mutanen ne a ranar 3 ga watan Fabrairu a yayin da jirgin ruwan ke kokarin barin ƙasar zuwa ƙasar Spain.
Oguntuga ya ce mutanen da aka kama matasa maza ne masu shekaru 24 zuwa 36 daga jihohin Delta, Edo, Imo, Ondo, Ekiti da Bayelsa, asai wani ɗan shekau 57 daga Delta.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama shugabar mata masu gurasa da suka yi zanga-zanga a Kano
“An gano su da kuma zaƙulo su abin yabawa ne, domin kuwa, kariya ce daga yiwuwar zamun barazanar tsaro ga jirgin da ma’aikatansa da kuma rayuwarsu a yayin wannan a teku ga jirgin da ma’aikatansa,” kamar yadda ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN)
Oguntuga ya ƙara da cewa an mika su ga Hukumar Shige-da-fice ta Najeriya (NIS) bisa ka’idojin da aka kafa domin ɗaukar matakin da ya dace.