An kama waɗanda suka kashe Janar ɗin Soja a Abuja

0
62
An kama waɗanda suka kashe Janar ɗin Soja a Abuja

An kama waɗanda suka kashe Janar ɗin Soja a Abuja

’Yan sanda sun kama ’yan fashin da ake zargi da kashe wani tsohon soja mai mukamin Birgediya-Janar a Abuja.

Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, Benneth Igweh, ne ya gabatar da wadanada aka zargin da kashe Birgediya-Janar Uwem Udukwere a gidansa da ke Abuja.

A ranar Asabar ne ’yan fashi suka kutsa gidan Birgediya-Janar Uwem Udukwere da ke rukunin gidajen Sunshine Estate, da misalin karfe 3 na dare suka hallaka shi.

KU KUMA KARANTA: Wani harin haɗin-gwiwa na Amurka da Birtaniya ya kashe mutum biyu a Yemen

Kwamishinan ’yan sandan ya bayyana cewa bindigar janar ɗin sojan da aka kashe na hannun ’yan fashin biyu da su tsere, waɗanda yanzu ake nema ruwa a jallo.

Leave a Reply