An kama wata malama da laifin yin lalata da ɗalibanta
Wata kotu a birnin Manchester ta samu wata malamar makaranta da laifin yin lalata da wasu ɗalibanta maza guda biyu.
An samu Rebecca Joynes, mai shekara 30, da laifukan lalata da ƙananan yaran har sau bibbiyu kowannesu.
An shaida wa alƙalin cewa hukumar makarantar ta kori malamar, saboda yin lalata da yaro na farko, sai kuma ta sake yi da yaro na biyu a lokacin da ake tsaka da tuhumarta.
Malama Joynes ta samu juna-biyu sakamakon lalata da yaron na biyun duk da cewa yana da ƙananan shekaru.
Malamar ta faɗa wa yaron cewa ba ta tsammanin za ta ɗauki ciki sakamakon lalatar.
KU KUMA KARANTA: An kama malami kan lalata da ɗaliba a Jami’ar Nsukka
An shaida wa kotun cewa malamar ta ja hankalin yaron ne mai shekara 15, ta hanyar saya masa wata belet (belt) mai ɗan karen tsada da ta kai fam 345, kafin ta yi lalata da shi a gidanta.
Ƙwararrun masu binciken kimiyya sun gano ƙwararan hujjojin aikata lalata a kan gadon malamar.
A lokacin da lamarin ya faru hukumar makarantar da takadar da malamar, yayin da ‘yan sandasuka ƙaddamar da bincike.
Da farko an bayar da belinta sakamakon gaza samun hujjar alaƙarta da yaron da bai kai shekara 18 ba.
To amma daga bisani sai ‘yan sanda suka gano cewa ta jima tana alaƙa da wani ɗalibin da suka ayyana a matsayin yaro.
A karon farko yaron ya taɓa zuwa gidanta a lokacin yana mai shekara 15, haka kuma bayan ya cika 16, ya sake komawa gidan suka sake aikata lalata da malamar, lamarin da ya sa ta samu juna-biyu.