An kama wasu manyan ɓarayin wayar salula da POS guda huɗu

0
218

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta damƙe wasu mashahuran ɓarayin POS da wayar salula su huɗu a ƙaramar hukumar Kazaure da ke jihar Jigawa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Isah, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba, 2023, ya ce waɗanda ake zargin sun amsa cewa sun shafe shekaru huɗu suna aikin.

A cewar PPRO, waɗanda ake zargin waɗanda kuma suka ƙware wajen fasa gidaje da sata, sun addabi al’ummar Kanti, Katoge, da Shagari Quarters duk a cikin babban birnin Kazaure.

Ya ce wadanda aka kama sun haɗa da 
 “Najib Murtala ‘m’ ɗan shekara 23 a Galandi Quarters tare da wasu guda uku (3), kuma an same su da na’urar P.O.S, da wayoyin hannu guda biyu (2) na android”.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda a Bauchi sun damƙe ɓarawon da ya saci mota a wani Masallaci a Zariya

“Bincike ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun ƙware wajen fasa gidaje da sata kuma sun addabi al’ummar Kanti, Katoge, da Shagari Quarters duk a cikin babban birnin Kazaure”.

“Dukkan  waɗanda ake zargin za a gurfanar da su a gaban kotu bayan gudanar da bincike na gaskiya a sashin binciken manyan laifuka na jiha (SCID) Dutse”.

Leave a Reply