Jami’an hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA sun kama wasu makafi guda uku da ke gudanar da wata haramtacciyar hanyar safarar miyagun ƙwayoyi tsakanin Legas da Kano.
Wata sanarwa da Femi Babafemi, kakakin hukumar ya fitar ta ce, har yanzu wani makaho na ƙungiyar ana neman shi.
Babafemi ya ce asirin ƙungiyar ya tonu ne biyo bayan kama wani makaho mai suna Adamu Hassan mai shekaru 40 a hanyar Gwagwalada Abuja ɗauke da skunk 12kg a hanyarsa daga Legas zuwa Kano a ranar Asabar 28 ga watan Oktoba.
Sai dai bincike ya tabbatar da cewa kwata-kwata be san abin da ke cikin jakar da aka bashi ya kai shi Kano ba.
KU KUMA KARANTA: Makaho ya damfari wata mata naira miliyan 19, ya yi lalata da ‘yarta da jikarta
“Bisa aikin ya kai ga kama babban ɗan ƙungiyar, Bello Abubakar, mai shekaru 45, wanda shi ma makaho ne.
A cikin bayaninsa, Bello wanda ke da aure da ‘ya’ya biyar ya ce ya shafe shekaru 30 yana zaune a Legas amma ya fara sana’ar miyagun ƙwayoyi shekaru biyar da suka wuce.
Babafemi ya ce wani wanda ake zargin, Muktar Abubakar, mai shekaru 59, wanda shi ma makaho ne ya kwashe shekaru 40 yana zaune a Legas kuma ya auri mata uku da ‘ya’ya 14.
“Dukkanin Muktar Abubakar da Bello Abubakar sun haɗa gwiwa ne da wannan sana’ar, yayin da mutum na uku da ake tuhuma, Akilu Amadu, mai shekaru 25, shi ma makaho yana bayar da gudummawar kuɗi ga masu safarar miyagun ƙwayoyi, kuma shi ne ya kai wa Adamu kayan a tashar motan Legas za ta kawo a Kano.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Wani makaho wanda ake sa ran zai karɓi kayan a Kano, Malam Aminu a halin yanzu ba a san inda yake ba.”