Rundunar ‘yan sandan farin kaya ta NSCDC reshen jihar Kano ta cafke wani matashi mai suna Alkasim Ya’u mai shekaru 25 da haihuwa da laifin kashe mahaifinsa a Tudun Yola ‘C’ da ke ƙaramar hukumar Gwale a Kano.
Kwamandan hukumar NSCDC, Mohammed Falala, ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Kano a ranar Lahadi, 7 ga Janairu, 2024.
Falala ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 5 ga watan Janairu, 2024 da misalin karfe 1330 a gidan Salisu Bala.
Mahaifin marigayin, Alhaji Ya’u Mohammed, ya kawo ɗansa mai taɓin hankali, Alkasim Ya’u, zuwa asibitin mahaukata na Dawanau, domin jinya, inda suka ɗauki takardar ganin likita a ranar Asabar 6 ga watan Janairu.
Ya bayyana cewa, maimakon ya koma Katsina, marigayin ya yanke shawarar kwana a gidan ɗan uwansa a adireshin ɗaya.
KU KUMA KARANTA: ’Yan bindiga sun kashe ɗan uwan amarya, sun sace mahalarta biki a Kaduna
“Binciken da muka gudanar ya nuna cewa Alkasim ya kamu da taɓin hankali ne sakamakon yadda yake gudanar da ayyukan ta’addanci,” in ji shi.
“A lokacin da suka isa Tudun Yola, ɗan mara lafiyar ya ɗauki wani abu mai kaifi ya raunata mahaifin, har sai da jami’an NSCDC da ke yankin suka shiga tsakani suka kai wanda aka kashen asibiti suka kama wanda ake zargin,” inji shi.
Falala ya ce tuni ‘yan uwa suka fara shirye-shiryen mayar da gawar Katsina domin yi mishi jana’iza, yayin da aka miƙa wanda ake zargin ga ofishin ‘yan sanda na Rijiyar Zaki domin ci gaba da bincike.
Kalli bidiyon a nan: