Connect with us

Labarai

An kama wani matashi ɗan shekara 25 da laifin kashe mahaifinsa da wuƙa a Kano (Bidiyo)

Published

on

Rundunar ‘yan sandan farin kaya ta NSCDC reshen jihar Kano ta cafke wani matashi mai suna Alkasim Ya’u mai shekaru 25 da haihuwa da laifin kashe mahaifinsa ​​a Tudun Yola ‘C’ da ke ƙaramar hukumar Gwale a Kano.

Kwamandan hukumar NSCDC, Mohammed Falala, ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Kano a ranar Lahadi, 7 ga Janairu, 2024.

Falala ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 5 ga watan Janairu, 2024 da misalin karfe 1330 a gidan Salisu Bala.

Mahaifin marigayin, Alhaji Ya’u Mohammed, ya kawo ɗansa mai taɓin hankali, Alkasim Ya’u, zuwa asibitin mahaukata na Dawanau, domin jinya, inda suka ɗauki takardar ganin likita a ranar Asabar 6 ga watan Janairu.

Ya bayyana cewa, maimakon ya koma Katsina, marigayin ya yanke shawarar kwana a gidan ɗan uwansa a adireshin ɗaya.

KU KUMA KARANTA: ’Yan bindiga sun kashe ɗan uwan amarya, sun sace mahalarta biki a Kaduna

“Binciken da muka gudanar ya nuna cewa Alkasim ya kamu da taɓin hankali ne sakamakon yadda yake gudanar da ayyukan ta’addanci,” in ji shi.

“A lokacin da suka isa Tudun Yola, ɗan mara lafiyar ya ɗauki wani abu mai kaifi ya raunata mahaifin, har sai da jami’an NSCDC da ke yankin suka shiga tsakani suka kai wanda aka kashen asibiti suka kama wanda ake zargin,” inji shi.

Falala ya ce tuni ‘yan uwa suka fara shirye-shiryen mayar da gawar Katsina domin yi mishi jana’iza, yayin da aka miƙa wanda ake zargin ga ofishin ‘yan sanda na Rijiyar Zaki domin ci gaba da bincike.

Kalli bidiyon a nan:

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Tinubu na shirin zuba tiriliyan 2 don bunƙasa tattalin arziki

Published

on

Tinubu na shirin zuba tiriliyan 2 don bunƙasa tattalin arziki

Tinubu na shirin zuba tiriliyan 2 don bunƙasa tattalin arziki

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya umarci tawagarsa ta tattalin arzikin ƙasar su shirya wani tsari na zuba naira tiriliyan biyu, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.33 don magance matsalolin da ake da su game da samar da abinci da hauhauwar farashi da kuma ƙarfafa muhimman sassa, in ji Ministan Kuɗi a ranar Alhamis.

Shirin, wanda za a aiwatar da shi tare da haɗin gwiwar gwamnatocin jihohi da kamfanoni masu zaman kansu, zai ware naira tiriliyan ɗaya, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 664.45 ga harkokin noma da samar da abinci da kuma bangaren makamashi, sai wata naira biliyan 350 domin kula da lafiya da walwalar jama’a, kamar yadda Olawale Edun ya fadawa manema labarai.

Tun bayan hawansa mulki a watan Mayun bara, Tinubu ya aiwatar da sauye-sauye da suka haɗa da rage tallafin man fetur da wutar lantarki da kuma rage darajar Naira sau biyu, a yayin da yake fafutukar ƙara zuba jari da ƙara yawan kayayyakin da ake samarwa.

KU KUMA KARANTA: Ɗangote ya soki sabon tsarin gwamnatin Tinubu

Sai dai tattalin arzikin ƙasar ba ya samun ci gaba cikin sauri ƙasa da 6% a duk shekara kamar yadda ya yi fata, yayin da sauye-sauyen suka sa tashin farashin kayayyaki ya kai mafi muni a cikin shekara 28, ya kuma ta’azzara yanayin rayuwa.

“Abu na farko da shugaban ya mayar da hankali a kai shi ne samar da abinci” a cewar Edun ranar Laraba bayan da Tinubu ya ƙaddamar da wani gyara na tsarin tafiyar da tattalin arziki.

Edun ya ce “Jajircewa wajen samar da abinci a farashi mai rahusa da kuma samar da shi da yawa shi ne abin da Shugaban Ƙasa ya fi mayar da hankali a wannan lokaci.”

Har ila yau, shirin na son magance matsalar raguwar yawan man da ake haƙowa da nufin ƙara yawansa zuwa ganga miliyan biyu a kowace rana, ta yadda za a samar da ƙarin kuɗaɗen shiga da kuma musayar kuɗaɗen waje ga tattalin arzikin ƙasar.

Najeriya ta dogara ne da man fetur wajen samun fiye da rabin kuɗaɗen shigarta da kuma kusan kashi 90% na kuɗin waje.

Sai dai yawan man da ake hakowa ya ragu a shekarun baya-bayan nan, inda satar man da zagon kasa da kuma ficewar manyan kamfanoni daga wuraren da ake haƙo man saboda matsalar rashin tsaro, inda suke mayar da hankali kan binciken mai a teku.

Edun bai fayyace lokacin aiwatar da shirin bunƙasa tattalin arzikin ba.

Continue Reading

Labarai

A fara duban watan sabuwar shekarar Musulunci – Sarkin Musulmi

Published

on

A fara duban watan sabuwar shekarar Musulunci - Sarkin Musulmi

A fara duban watan sabuwar shekarar Musulunci – Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya umarci al’umma da su soma duban watan Muharram na Sabuwar Shekarar musulunci ta 1446 Hijiriyya daga ranar Jumu’a 5 ga watan Yuli, 2024.

A madadin Sarkin Musulmi, Wazirin Sakkwato kuma Shugaban Kwamitin Bayar da Shawara kan Harkokin Addini a Masarautar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaid, ne ya fitar da sanarwar.

Farfesa Sambo, ya ce duk wanda ya samu ganin watan ya sanar da Majalisar Sarkin Musulmi ko wani uban kasa ko hakimi domin sanar da al’umma.

KU KUMA KARANTA: Dole mu kare martabar Sarkin Musulmi – Kashim Shettima

Watan Muharram shi ne watan farko a tsarin watanni 12 na Shekarar musulunci.

Idan an ga watan, Asabar 6 ga watan Yuli, 2024, zai kasance ranar farko a shekarar 1446 Hijiriyya.

Continue Reading

Labarai

‘Yan ta’adda sun kashe mutane sama da mutum 7,000 a Yammacin Afirka a bana – Tuggar

Published

on

‘Yan ta’adda sun kashe mutane sama da mutum 7,000 a Yammacin Afirka a bana - Tuggar

‘Yan ta’adda sun kashe mutane sama da mutum 7,000 a Yammacin Afirka a bana – Tuggar

Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ya bayyana buƙatar gaggawa wajen haɗa kai don yaƙi da ta’addanci da sauran matsaloli na rashin tsaro a Yammacin Afirka.

A saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Tuggar ya ce daga watan Janairu zuwa watan Mayun 2024, an samu hare-haren ‘yan ta’adda 800 a Yammacin Afirka, musamman a ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar.

Ya ƙara da cewa sama da mutane 7,000 ne suka mutu sakamakon hare-haren na ta’addanci a yankin.

KU KUMA KARANTA: Bai kamata ƴan ba-ni-na-iya su shigo da matsalolinsu Gabas ta Tsakiya ba – Turkiyya

“Dole ne mu haɗa kai waje guda don magance matsalolin tsaro, kuma mu yi aiki ba gajiyawa domin tabbatar da tsaro, dimokuraɗiyya da cigaban yankinmu,” in ji Tuggar.

Ya ƙara da cewar a yayin taron, sun kuma sake nazari da duba kan Tsarin Dimokuraɗiyya da Shugabanci na ECOWAS, inda ya kuma yaba da ayyukan samar da zaman lafiya da taimakon jinƙai da ake bayarwa a yankin.

Ƙasashen Yammacin Afirka dai suna fama da hare-hare na ƙungiyoyin da ke da alaƙa da ISIS da Boko Haram ko ISWAP.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like