No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar sojojin Najeriya Brigade ta 9, da ke Ikeja Cantonment a jihar Legas, ta kama wasu mutane biyar da ke yin sojin bogi. 

Waɗanda ake zargin da aka miƙa wa ‘yan sanda domin ci gaba da bincike da gurfanar da su a gaban Kotu, an ce an kama su a lokuta daban-daban a yankunan Ojodu Berger, Ikorodu, Ogba, da Ikeja a Legas.

KU KUMA KARANTA: An cafke Kwamishinan ‘yan sanda na bogi a Legas

Waɗanda ake zargin dai sun haɗa da Johnson Ayemoba, Salami Olamilekan, Mumammed Bilyaminu, Abijo Taofeek, da Adewale Quadri, a cewar daraktan hulɗa da jama’a na rundunar ta 9, Manjo Augustine Kolawole, an kama su ne a wani sintiri na yau da kullum da rundunar ta Brigade ta yi.

Tuni rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta fara bincike domin gurfanar da sojojin bogi da soji suka kama suka miƙa mata.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...