‘Yansanda a Adamawa, sun kama saurayi da budurwa da su ka yi garkuwa da kansu

0
198
An kama saurayi da budurwa da su ka yi garkuwa da kansu a jihar Anambra

‘Yansanda a Adamawa, sun kama saurayi da budurwa da su ka yi garkuwa da kansu

Rundunar ‘Yansandan Jihar Anambra ta kama saurayi da budurwa da suka kitsa sace kansu da kansu tare da kwato kuɗin fansa naira miliyan ₦1.2 da iyalan wanda ake cewa an sace suka biya tun da fari.

A cewar sanarwar da kakakin rundunar, SP Tochukwu Ikenga, ya fitar a ranar Asabar, wadanda aka kama su ne Nmesoma Nwoye, ‘yar shekara 23, da saurayinta Chibuike Ogbu, mai shekara 24. An cafke su ne bayan binciken sirri ya gano cewa Nmesoma ta hada baki da saurayinta domin shirya sace kanta.

Ikenga ya bayyana cewa da farko sun bukaci kuɗin fansa naira miliyan ₦15, amma daga baya bayan tattaunawa aka tura ₦3m zuwa asusun bankin Nmesoma.

Ya ce bayan kama su, Kwamishinan ‘Yansanda na jihar, CP Ikioye Orutugu, ya nuna damuwarsa kan yawaitar lalacewar tarbiyya a cikin al’umma, inda ya kara da cewa jami’an rundunar Rapid Response Squad, Awkuzu ne suka kama su.

KU KUMA KARANTA: Rundunar ‘yansanda a Yobe ta kama wata mata da ake zargi ta kashe mijinta, sakamakon rikici a kan abinci

Sanarwar ta ce: “An gano wadanda ake zargi ,Nmesoma Josephine Nwoye, ‘yar shekara 23, da Chibuike Ogbu, mai shekara 24, inda binciken sirri ya tabbatar da cewa wadda ake cewa an sace ta hada baki da saurayinta domin kitsa wannan shiri.

“Jami’ai sun kuma kwato kuɗin fansa ₦1,200,000 da iyalan budurwar suka biya tun farko.

“Bincike ya nuna cewa wadanda ake zargi sun fara bukatar ₦15m a matsayin fansa, amma daga baya aka tura ₦3m cikin asusun budurwar.”

Leave a Reply