No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar tsaro ta Civil Defence Corp a Nijeriya ta ce ta kama aƙalla mutane 76 da ake zargi da yunƙurin yin auren jinsi a Jihar Gombe da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Mai magana da yawun rundunar reshen Jihar Gombe SC Buhari Sa’ad ne ya bayyana haka a ranar Lahadi inda ya ce sun samu nasarar kama matasan ne bayan sun samu bayanan sirri cewa suna shirin wani biki na zagayowar ranar haihuwa da kuma auren jinsi.

Sa’ad ya shaida wa manema labarai cewa cikin mutane 76 da ake zargi, 59 maza ne inda 21 daga cikinsu suka tabbatar da cewa su ‘yan luwaɗi ne sai kuma akwai mata 17 waɗanda aka kama a wurin.

Ya ce da zarar an kammala bincike za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.

KU KUMA KARANTA: Hukumar Hisbah a Kano ta kama wasu mutane biyu bisa zarginsu da auren jinsi

Ba wannan ne karon farko da ake kama masu yunƙurin auren jinsi ba a Nijeriya domin ko a watan Yulin bana sai da hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wasu da ake zargi da auren jinsi.

Haka ma a watan Agustan da ya gabata rundunar ‘yan sandan Jihar Delta ta kama sama da mutum 100 waɗanda ake zarginsu da auren jinsi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...