An kama mutum 34 lokacin zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Amurka

0
151

Adadin masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu da aka kama a yayin wata zanga-zanga a Jami’ar Texas ta Amurka ya kai 34, a cewar hukumomi.

“Ya zuwa karfe 9 na dare, jami’an tsaro sun kama mutum 34 a harabar Jami’ar UT Austin biyo bayan zanga-zangar yau da aka gudanar,” a cewar wani sako da Ma’aikatar Tsaron Al’umma ta Texas ta wallafa a shafinta na X, wanda a baya ake kira Twitter, a ranar Laraba.

Daga cikin waɗanda aka kama har da wani mai ɗaukar hoto na gidan talabijin din FOX 7, Austin wanda ke ɗaukar hoton zanga-zangar daliban a harabar Jami’ar UT Austin.

Hotunan soshiyal midiya sun nuna yadda aka kwantar da mai ɗaukar hoton a ƙasa kana aka ɗaure masa hannayensa.

Ɗaliban sun gudanar da wani tattaki ne domin neman jami’ar ta janye kanta daga ƙera makaman da ke da alaƙa da Isra’ila.

KU KUMA: Ana ci gaba da kama masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu a jami’o’in Yale, NYU da ke Amurka

Zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tashin hankali bayan da dakarun Sashen Tsaron Al’umma na Texas suka kutsa kai cikin taron.

Tattakin wani ɓangare ne na zanga-zangar gama gari na nuna goyon baya ga Falasɗinu inda aka buƙaci cibiyoyin ilimi su janye daga kamfanonin da ke kasuwanci da Isra’ila.

Sai dai Ma’aikatar Tsaron al’umma DPS ta ce tana mayar da martani ne bisa ga buƙatar jami’ar da kuma Gwamna Greg Abbott.

Abbott ya ce za a ci gaba da kamen har sai taron ya watse.

Leave a Reply