Connect with us

Labarai

An kama mutane tara da zargin amfani da audugar mata da famfas wajen haɗa matashin-kai

Published

on

Hukumar tsaron farin kaya ta ƙasa, NSCDC, ta kama wasu mutane tara da suke haɗa wa da siyar da matashin kai da suke cika shi da famfas ɗin yara da audugar mata da akayi anfani da su a Sakwkwato.

Da ya ke gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar rundunar a ranar Laraba, kwamandan jihar, Bello Alkali Argungun, ya ce kamasu ya biyo bayan rahoton sirri da su ka samu.

Ya ce, “Sun yi amfani da yara ƙanana da suke kawo musu shara. Sun cika kwandon matashin kai da shi wanda suke sayar wa kwastomominsu. Kayan matashin kan na ɗauke da tambari daban-daban na sanannun kamfanonin yin katifa.”

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sandan Kano sun kama mutum tara bisa zargin su da sayar da yara

A cewar Argungun, hakan na iya yin illa ga lafiyar masu amfani da matashin kan.

“Suna iya kamuwa da wasu cututtuka ba tare da sanin musabbabin hakan ba. Ina ƙira ga jama’armu da su rika zuwa kasuwa da suka dace domin sayen kayayyaki,” inji shi

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Wani mutum ya yi barazanar kashe kansa kan tsadar rayuwa

Published

on

Wani mutum ya yi barazanar kashe kansa kan tsadar rayuwa

Wani mutum ya yi barazanar kashe kansa kan tsadar rayuwa

Daga Idris Umar, Zariya

An kuɓutar da wani mutum da ya hau saman dogon ƙarfen Sabis ɗin gidan rediyo yana yunƙurin kashe kansa ranar Litinin a Abuja.

Mutumin mai suna Shuaibu Yusuf, wanda ɗan asalin Jihar Borno ne, an kuɓutar da shi daga kan dogon ƙarfen bayan da jami’an agajin gaggawa suka yi ta roƙonsa da yayi haƙuri ya sauko, inda daga bisani ‘yan sanda suka kama shi.

Shu’aibu ya sha alwashin sadaukar da rayuwarsa domin al’amuran da ke damun al’ummar ƙasar, yayin da yake rokon ‘yan Najeriya da su ba shi haɗin kai, yana mai jaddada cewa a shirye ya ke ya sadaukar da rayuwarsa kan abubuwan da ya ƙira mummunan halin Rayuwa.

KU KUMA KARANTA: Muna ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban jami’ar da ‘yan bindiga suka sace – Gwamnatin Kogi

Ya buƙaci da a maido da tallafin man fetur, tare da ayyana dokar ta ɓaci kan rashin tsaro, sannan Gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa a Jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi, Katsina, Neja, da Borno domin yaƙar ta’addanci da kuma dawo da zaman lafiya.

Mutumin ya kuma buƙaci a buɗe kan iyakokin ƙasar nan domin shigo da abinci domin shawo kan matsalar karancin abinci, sannan kuma ya kamata Gwamnati ta magance matsalar yaran da ba sa zuwa Makaranta.

Mun sami rahoto cewa jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa NEMA da jami’an Babban Birnin Tarayya ne suka hallara domin kuɓutar da shi.

A cewar rahoton, mutumin ya hau kan ƙarfen Eriya da ake zargin na gidan rediyon Aso ne bayan ya ajiye takardar da ke bayyana manufarsa da buƙatunsa.

Masana sun tabbatar da cewa a baya-bayan nan ana samun karuwar al’ummar dake kasar dake kashe kawunansu saboda halin ƙunci da tsadar rayuwa da ake ciki.

Wasu masana harkokin kiwon lafiya sun ɗora alhakin yunkurin kashe kawunan da matsalar taɓarɓarewar tattalin arziki da yunwa a ciki da wajan ƙasar.

Continue Reading

Labarai

Kotu ta umarci Sadiya Farouq ta yi bayani kan yadda aka kashe biliyan N729 na tallafi

Published

on

Kotu ta umarci Sadiya Farouq ta yi bayani kan yadda aka kashe biliyan N729 na tallafi

Kotu ta umarci Sadiya Farouq ta yi bayani kan yadda aka kashe biliyan N729 na tallafi

Kotun Tarayyar da ke Legas ta umarci tsohuwar ministar ayyukan jin ƙai a gwamnatin Buhari wato Sadiya Umar-Farouq ta yi bayani kan yadda ta kashe naira biliyan 729 da gwamnatin ƙasar ta bai wa ‘yan Najeriya miliyan 24 a watanni shida na 2021.

Haka kuma kotun ta bayar da umarni ga tsohuwar ministar ta kawo jerin sunayen mutanen da aka biya kuɗin, da kuma jihohin da waɗanda aka biya kuɗin suka fito da kuma adadin da kowace jiha ta samu.

Ƙungiyar nan da ke yaƙi da cin hanci ta SERAP a Najeriya ce ta shigar da tsohuwar ministar ƙara inda ta buƙaci a yi bayani kan yadda aka raba kuɗin a zamanin Buhari.

Kotun ta bayyana cewa ƙungiyar da ta shigar da ƙarar ta buƙaci a ba ta bayanai dangane da kuɗin da aka raba wa ‘yan ƙasar a 2021.

Ƙungiyar ta SERAP ta yi jinjina ga hukuncin da alƙalin kotun Deinde Isaac Dipeolu ya yanke inda ya ce hakan “nasara ce ga gaskiya da riƙon amana wurin kashe kuɗaɗen jama’a.”

Tuni dai SERAP ɗin ta aika wasiƙa ga ofishin shugaban Nijeriya Bola Tinubu da kuma babban lauyan kasar domin su bi umarnin hukuncin da kotun ta yanke.

KU KUMA KARANTA: Shugabannin bankuna na amsa tambayoyi kan badaƙalar Beta Edu da Sadiya — EFCC

“Muna buƙatar ku umarci ma’aikatar jin kai da ta gaggauta tattara tare da fitar da bayanan kashe kudade na naira biliyan 729 (dala miliyan 467) kamar yadda kotu ta bayar da umarni,” in ji mataimakin daraktan ƙungiyar, Kolawole Oluwadare a ranar Asabar.

Continue Reading

'Yansanda

An ja hankalin ‘yan Najeriya kan shirin ƙungiyoyin asiri na ɗaukar sabbin mambobi

Published

on

An ja hankalin 'yan Najeriya kan shirin ƙungiyoyin asiri na ɗaukar sabbin mambobi

An ja hankalin ‘yan Najeriya kan shirin ƙungiyoyin asiri na ɗaukar sabbin mambobi

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ja hankalin ‘yan ƙasar game da shirin ƙungiyoyin asiri na ɗaukar sabbin mambobi a faɗin ƙasar musamman a jami’o’i da manyan makarantu.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Jihar Ribas Grace Iringe-Koko ce ta yi wannan jan hankali a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar da maraice a birnin Fatakwal.

Ta bayyana cewa wata babbar ƙungiyar asiri ta Najeriya tana shirin gudanar da gagarumin biki ranar Lahadi a faɗin Najeriya, musamman a jami’o’i don tunawa da mutumin da ya kafa ta.

“Rundunar ‘yan sandan Jihar Ribas ta samu bayanai game da bikin da ƙungiyar Neo-Black Movement (NBM) za ta yi a faɗin ƙasar ranar 7 ga watan Yulin 2024. Ƙungiyar, wadda ake yi wa laƙabi da Aiye ko Black Axe, tana shirin gudanar da bikin ne domin tunawa da wanda ya kafa ta.

KU KUMA KARANTA: Shugaban hukumar leƙen asirin sojin Isra’ila ya yi murabus saboda harin Hamas na 7 ga Oktoba      

Bikin, wanda aka sanya wa suna Ranar AIYE ko 7/7 za a gudanar da shi ne a dukkan jihohin da ke faɗin ƙasa, musamman a manyan makarantu,” in ji sanarwar.

An gargaɗi masu ta da hankalin jama’a a Bikin Dodanni na Egungun a Jihar Oyo

Rundunar ‘yan sandan ta ce tana sane da munanan ayyukan ƙungiyar asirin na kisan mutane a manyan makarantu da faɗace-faɗace a tsakanin ƙungiyoyin asiri da tayar da zaune-tsaye da sauran manyan laifuka.

Ta ce yanzu haka ta baza ƙarin jami’an ‘yan sanda zuwa wasu wurare domin daƙile ayyukan ƙungiyoyin asiri, sannan ta yi ƙira ga iyaye su gargaɗi ‘ya’yansu su guji shiga ayyukan ƙungiyoyin asiri.

“Ana bai wa manyan makarantu shawarar ƙara matakan tsaro da kuma sanya idanu sosai domin tabbatar da tsaron dukkan ɗalibai.

Kazalika ana ƙira ga dukkan makarantu su lura da duk wani taro na ɗalibai da bai kwanta musu a rai ba,” a cewar sanarwar.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like