Hukumar tsaron farin kaya ta ƙasa, NSCDC, ta kama wasu mutane tara da suke haɗa wa da siyar da matashin kai da suke cika shi da famfas ɗin yara da audugar mata da akayi anfani da su a Sakwkwato.
Da ya ke gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar rundunar a ranar Laraba, kwamandan jihar, Bello Alkali Argungun, ya ce kamasu ya biyo bayan rahoton sirri da su ka samu.
Ya ce, “Sun yi amfani da yara ƙanana da suke kawo musu shara. Sun cika kwandon matashin kai da shi wanda suke sayar wa kwastomominsu. Kayan matashin kan na ɗauke da tambari daban-daban na sanannun kamfanonin yin katifa.”
KU KUMA KARANTA: ‘Yan sandan Kano sun kama mutum tara bisa zargin su da sayar da yara
A cewar Argungun, hakan na iya yin illa ga lafiyar masu amfani da matashin kan.
“Suna iya kamuwa da wasu cututtuka ba tare da sanin musabbabin hakan ba. Ina ƙira ga jama’armu da su rika zuwa kasuwa da suka dace domin sayen kayayyaki,” inji shi