An kama matashin da ya sace wa mai sana’ar POS dubu ɗari tara a Jigawa

0
194

Daga Ibraheem El-Tafseer

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wani yaro ɗan shekara 17 mai suna Abdulmuminu Tasiu bisa laifin damfarar wani mai sana’ar POS kuɗi naira dubu ɗari tara a ƙaramar hukumar Maigatari.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

A cewar sanarwar, “Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a inda wani mai suna Aminu Mustafa mai shekaru 38 a unguwar Dodo da ke ƙaramar hukumar Maigatari mai sana’ar POS ya baiwa wani abokin ciniki injin (POS machine) ya shigar da lambar sirrinsa domin a cire masa kuɗi, shi ne ya sace masa Naira dubu ɗari tara.

“Mai sana’ar POS ɗin ya kai rahoto ga ‘yan sanda cewa wani da ba a san ko wanene ba ya zo shagon sa na POS ya ciro kuɗi wanda bayan ya ba shi na’urar POS ya yi amfani ta hanyar damfara sannan ya tura kuɗi naira dubu dari tara (N900,000) a asusun sa.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda a Gwambe, sun kama matashin da ya kashe wata mata mai shekaru 58

“Da samun bayanan, an sanar da ‘yan sandan da ke sintiri, an yi sa’a, an kama Abdulmuminu Tasi’u ɗan shekara 17, wanda ke Adakawa quarters, ƙaramar hukumar Dala Kano, aka kawo shi ofishin domin bincike.”

Shiisu ya ce da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amince da aikata laifin.

Ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu bayan an gudanar da bincike.

Leave a Reply