An kama matashi kan zargin luwaɗi da ɗan shekara 4 a Gombe

0
214

An kama wani matashi da ake zargi da aikata luwaɗi da wani ƙaramin yaro ɗan shekara huɗu a ƙaramar hukumar Balanga ta jihar Gombe.

Bayanai sun ce wasu ƙwararrun mafarauta ne suka cafke mutumin da ake zargi a ƙaramar hukumar.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ASP Mahid Mu’azu Abubakar ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Ya bayyana cewa mafarautan sun kama wanda ake zargin ne a lokacin da jama’a ke ƙoƙarin ɗaukar doka a hannunsu bayan kama shi da aka yi dumu-dumu yana luwaɗi da yaron.

Mahid, ya ce da misalin ƙarfe 8 na dare ne aka kama wanda ake zargin, wanda kuma aka mika wa jami’an ’yan sanda domin ɗaukar matakin da ya dace.

KU KUMA KARANTA: An cafke jami’in gidan yari kan zargin luwaɗi da ƙaramin yaro a Gwambe

Kakakin ’yan sandan ya ce an garzaya da yaron asibitin domin duba lafiyarsa, a yayin da ’yan sanda ke ci gaba da gudanar da binciki domin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

Kazalika, ASP Mahid ya ce rundunar ’yan sandan ta kama wasu mutum 4 mazauna unguwar London mai Dorawa da suka kware wajen ta’adar sace-sace a gidajen jama’a a Gombe.

Kakakin rundunar ’yan sandan ya ce a ranar 14 ga watan Nuwamba ne jami’an haɗin gwiwa na Operation Hattara suka kama su a wani lokacin da suke sintiri a unguwar.

Ya ce barayin sun fasa gidaje biyar a unguwar Zagaina, inda suka yi nasarar sace babura 6 a lokuta daban daban.

A cewarsa, bincike ya yi zurfi a kan lamarin kuma da zarar sun kammala za su tura su zuwa kotu domin su fuskanci hukunci.

Leave a Reply