No menu items!

Sample Page Title

Date:

Daga; Rabo Haladu.

RUNDUNAR ƴan sandan Jihar Kano, ta tabbatar da kama wata tsohuwa da ake zargin ta saka wani matashi mai shekara 17 ya ƙwaƙulewa wani yaro mai suna Mustapha Dahiru ido don a haɗa musu layar zana.

Rundunar ƴan sanda ta ce ta kamo matar ne bayan koke da suka samu daga Jama’ar unguwa da ƴan sa kai na yankin unguwar Dan Tsinke a karamar hukumar Tarauni a Kano.

Tun kafin ƴan sanda su kai ga kamo matar da ake zargi da sa matashin ya cirewa yaron ido, kungiyar tsaro ta ‘yan sa-kai ta Dan Tsinke da ke kusa da Unguwar Sheka suka kamo matashin da ake zargi da cirewa yaron idon

Matashin da ake zargi ya shaida musu cewar wata tsohuwa ce ta umarci da ya kawo mata ido don ta hada masa layar zana, kamar yadda Rabi’u Suleiman Mai Matasa mataimakin sakatare na kungiyar ‘yan-sa kai ta Dan Tsinke a Kano ya ce.

SP Abdullahi Kiyawa kakakin ƴan sanda a Kano, ya tabbatar da faruwar al’amarin, ya kuma ja hankulan al’umma da su ringa sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a kewayen su, don kaucewa afkuwar irin wannan lamari.

Ko a makon da ya gabata sai da aka sami wani matashi da ya tura ‘yar uwarsa a cikin rijiya, a yankin karamar hukumar Rimin Gado a Kano, tare da wani matashi da ya kashe wata yarinya, yar makwabcin gidansu, bayan da ya nemi kudin fansa.

admin
adminhttps://neptuneprimehausa.com
Ni ɗan jarida ne mai zaman kansa. Mawallafi kuma mai sharhi a lamarin yau da kullum.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...