An kama masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Chicago

0
73
An kama masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Chicago

An kama masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Chicago

An kama gomman masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a wajen ƙaramin ofishin jakadancin Isra’ila da ke Amurka da kuma kan titunan birnin Chicago a dare na biyu na taron tsayar da ‘yar takarar shugaban ƙasa ta jam’iyyar Democrat.

An yi arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro, bayan da wasu daga cikin masu zanga-zangar, sanye da baƙaken tufafi kuma fuskokinsu a rufe, suka matsa kusa da shingen da ‘yan sanda suka sanya don hana su isa wurin taron.

KU KUMA KARANTA: Ba mu da labarin rasa rai a lokacin zanga-zanga – ‘Yan sandan Kano

Wani mai zanga-zanga sanye da hular Chicago Bulls, wanda ya rufe fuskanrsa, ya yi kira ga masu zanga-zangar su “hana taron DNC.”

Ƙungiyar da ta gudanar da zanga-zangar, wadda ba ta da alaƙa da gamayyar ƙungiyoyi fiye da 200 da suka yi zanga-zanga ranar Litinin ɗin da ta gabata, ta sanya wa zanga-zangar taken “Make it great like ’68,” domin nuna irin zanga-zangar da aka yi a ƙasar don yin hamayya da Yaƙin Vietnam a yayin taron ƙasa na jam’iyyar Democrat na shekarar 1968.

Leave a Reply