No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Abiya, ta ce ta cafke wani jami’in ‘yan sanda da aka kora, Francis William, a lokacin da yake yunƙurin satar taransifoma na kamfanin wutar lantarki na Aba da ke National High School Port-Harcourt, Aba.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Kenechukwu Onwuemelie ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba, 2023, yayin da yake zantawa da manema labarai a Umuahia kan ayyuka da nasarorin da rundunar ta samu daga watan Yuli zuwa Satumba.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama waɗanda ake zargi da sace ɗaliban jami’a a Najeriya

CP Onwuemelie, wanda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Maureen Chinaka ya wakilta, ya ce jami’an tsaro daga hedikwatar ‘yan sanda na Ndiegoro, Aba, sun kama William, mai shekaru 34, da misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar 11 ga watan Satumba.

Ya ce an kama mutumin ne sanye da tufafin ‘yan sanda, da hular facing cap, kuma yana riƙe da katin shaidar ‘yan sanda na bogi.

“An kama shi, kuma an ƙwato dukiyar da ya sace, an gurfanar da shi a gaban kotu, kuma an tsare wanda ake zargin a gidan yari,” inji shi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...