An kama jirgin ruwa ɗauke da ‘yan ci-rani sama da 200 da ke hanyar zuwa Turai

0
90
An kama jirgin ruwa ɗauke da 'yan ci-rani sama da 200 da ke hanyar zuwa Turai

An kama jirgin ruwa ɗauke da ‘yan ci-rani sama da 200 da ke hanyar zuwa Turai

Rundunar Sojin Senegal a ranar Asabar ta ce ta kama wani jirgin ruwa wanda ke ɗauke da ‘yan ci-rani sama da 200 waɗanda ke hanyarsu ta zuwa Turai.

A wata sanarwa da sojojin suka fitar a shafinsu na X, sun bayyana cewa wani jirgin ruwan soji wanda ke shawagi ne ya gano jirgin a ranar Juma’a ɗauke da mutum 202, daga ciki har da mata biyar da ƙaramin yaro.

A farkon watan Yulin nan, wani jirgin ruwa ɗauke da kusan mutum 170 wanda ya bar Senegal zuwa Mauritania ya kashe kusan mutum 90 bayan ya kife.

Wannan bala’in ne ya jawo Firaiministan Senegal Ousmane Sonko ya yi magana da babbar murya inda ya roƙi mutane da su daina kasada suna sayar da rayuwarsu ta hanyar shiga irin waɗannan jiragen ruwan masu cunkoso.

Sai dai duk da haka masu tafiya ci-ranin zuwa Turai a halin yanzu suna ƙara bin wannan hanya duk da yadda ake ƙara tsaurara tsaro a cikin tekun.

KU KUMA KARANTA: Wani jirgin ruwa ya kife da ‘yan ci-rani a tekun Mauritania

“Ina sake kira ga matasa: ba za ku magance matsalolinku a cikin jirgin ruwa ba,” kamar yadda Sonko ya shaida wa taron wasu matasa a Saint-Louis.

“Makomar duniyar nan ita ce Afirka… wadda ita ce nahiyar da har yanzu take da akamun samun ci gaba.”

Kamar yadda wata ƙungiya mai zaman kanta ta Sifaniya Caminando Fronteras ta bayyana, sama da mutum 5,000 suka rasua hanyarsu ta zuwa Sifaniya ta teku a watanni biyar na farkon wannan shekarar, wanda wannan shi ne adadi mafi yawa tun bayan da ƙungiyar ta soma aikin tattara alƙaluma a 2007.