Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta ce ta kama wani ƙasurgumin ɗan bindiga wanda ya shaida mata cewa ya yi ƙaura ne daga jihar Kaduna zuwa Kano don ya kafa sansanin ƴan bindiga a dajin Gwarzo zuwa Ƙaraye.
Sanarwar da rundunar ta fitar a ranar Litinin da maraice mai ɗauke da sa hannun mataimakin jami’in hulɗa da jama’a ASP Abdullahi Hussaini ta ce wata tawagar ƴan sanda da ke aikin leƙen asiri ce ta kama mutumin.
“A ranar 4 ga wata ne da misalin ƙarfe 5.40 na yamma, wata tawagar ƴan sanda da ke aikin leƙen asiri a ƙaramar hukumar Ƙaraye ƙarƙashin jagorancin SP Aliyu Mohammed Auwal, ta yi nasarar kama Isah Lawal mai shekara 33 ɗan asalin ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna,” in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa an kuma samu shanu 55 da tumaki shida a wurinsa a samamen da ƴan sandan suka yi a kan iyakar jihohin biyu.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama shugabar mata masu gurasa da suka yi zanga-zanga a Kano
“A yayin bincike ne wanda ake zargin ya bayyana cewa sun gudu ne daga Sansanin Ƴan Bindiga na Maidaro a ƙaramar hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna saboda an kashe shugabansu Bashir, ɗan garin Malumfashi na Jihar Katsina a wani faɗa tsakanin ƙungiyoyin ƴan bindiga biyu da aka yi.
“Ya ce wannan ne dalilin da ya sa suka tsere zuwa Jihar Kano don kafa sabon sansani a Dajin Gwarzo zuwa Ƙaraye,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Rundunar ƴan sandan ta ce yanzu haka an gudanar da wani bincike na musamman a kan mutumin, wanda ke bayar da bayanai masu muhimmanci da za su taimaka wa ƴan sanda daƙile matsalar fashi da satar mutane a maƙwabtan jihohi.
Kwamishinan ƴan sanda na Jihar Kano Mohammed Usaini Gumel ya yaba wa jami’an da suka yi wannan ƙoƙari tare da bayar da umarnin samar da ƙarin kayan aiki da jami’ai don ci gaba da bincike da shawo kan matsalar.
Jihohin yankin arewa maso yammacin Najeriya da suka haɗa da Katsina da Kaduna, waɗanda ke maƙwabtaka da Kano, da kuma Zamfara da Sokoto da Kebbi har ma da Neja da ke arewa ta tsakiya, na fama da matsalar ƴan bindiga da masu satar mutane don karɓar kudin fansa.
An shafe shekaru ana fama da matsalar kuma tana sake ta’azzara kamar yadda masu sharhi kan tsaro ke cewa.
Sai dai hukumomin ƙasar suna yawan bayyana nasarar da suke samu ta murƙushe ƴan bindigar, inda wasu jihohin ma suka fara samar da rundunonin tsaro na cikin gida don daƙile ƙalubalen, wanda ya durƙusar da harkokin yau da kullum da yawa musamman fannin noma.