No menu items!

Sample Page Title

Date:

Kotu ta tsare wasu mutum biyar a gidan yari kan zargin satar jariya ’yar kwana takwas domin yin tsafi a Kano

Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Gama PRP a Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare wasu mutane biyar a gidan yari kan yunƙurin satar wata jaririya ’yar kwanaki takwas da haihuwa domin yin tsafi da ita.

Mai gabatar da ƙara Aliyul Abidin ya shaida wa kotun cewa waɗanda ake tuhuma sun haɗa baki domin sace jaririyar wacce ake zargin tsafi za a yi da ita, su kuma za a biya su Naira miliyan 30 a matsayin ladan aikinsu.

Sai dai maza biyu daga cikin waɗanda ake zargi sun musanta laifukan, a yayin da sauran ukun da ake zargi kuma suka amsa laifin.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun cafke wata mata bisa zargin satar jariri a asibiti a Legas

Alƙalin kotun Mai sharia Nura Yusuf Ahmad ya bayar da umarnin tsare dukkansu, maza huɗu da mace ɗaya a gidan gyaran hali tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Oktoba, 2023.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...