Connect with us

Laifi

An kama ɓarawon da ya addabi mutane da satar babura a bakin ‘Union Bank’ da ke Kano

Published

on

Jama’ar unguwar Sharaɗa sun cafke wani matashi mai suna Jibrin Rimin keɓe a Kano, a lokacin da yake ƙoƙarin satar Babur a bankin Union Bank dake Sharaɗa a ranar Alhamis.

Matashin ya bayyana cewa abokinsa mai suna Sadik mazaunin Zoo road Kano ne ya koya masa saƙar a mungun zare.

Sai dai ya ce idan ya saci Babur ɗin suna kaiwa wani mai suna Haruna da aka fi sani da Mallam Tijjani Kurna, inda yake sayan kowanne babur ɗaya kan naira dubu tamanin ko dubu ɗari.

Wanda ake zargi ya ƙara da cewa, sun daɗe suna aikata wannan aika-aikar a sassan jahar Kano tsawon lokaci.

Tuni dai aka damƙa matashin a ofishin ‘yan sanda na Sharaɗa kamar yadda majiyar mu ta tabbatar mana.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

'Yan bindiga

‘Yan bindiga sun kashe malamin jami’a a Katsina, sun sace ‘ya’yansa

Published

on

'Yan bindiga sun kashe malamin jami'a a Katsina, sun sace 'ya'yansa

‘Yan bindiga sun kashe malamin jami’a a Katsina, sun sace ‘ya’yansa

Rahotanni daga Jihar Katsina  na cewa ‘yan bindiga sun kashe wani malamin Jami’ar Tarayya ta Dutsinma.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da tsakar dare da misalin ƙarfe 1:30 inda ‘yan bindigar suka afka gidan Dakta Tiri Gyan da ke Yarima Quarters a Ƙaramar Hukumar Dutsinma.
Mai magana da yawun ‘yan sandan  reshen Katsina Abubakar Sadiq ya tabbatar wa kafar watsa labarai ta Channels  da kisan malamin.

Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun afka gidan malamin jami’ar da makamai daban-daban inda suka yi ta harbi domin tsorata mazauna rukunin gidajen.

Sun kuma bayyana cewa ɓarayin sun sace yara biyu na Dakta Gyan a lokacin da suka kai harin.

KU KUMA KARANTA: ’Yan bindiga sun sace Hakimi da manoma 2 a Kaduna

Kashe malamin na zuwa ne mako guda bayan kashe mataimakin Shugaban Jami’ar Usman Ɗanfodiyo da ke Sokoto Farfesa Yusuf Saidu.

An kashe shi a lokacin da yake hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Sokoto.

Continue Reading

Laifi

Wani uba ya yi wa ’yarsa mai shekara 8 fyaɗe

Published

on

Wani uba ya yi wa ’yarsa mai shekara 8 fyaɗe

Wani uba ya yi wa ’yarsa mai shekara 8 fyaɗe

Wani mai sayar da maganin gargajiya ya gurfana a gaban kotu bisa zarginsa da yi wa ɗiyarsa mai shekaru takwas fyaɗe.

An gurfanar da magidancin mai shekaru 35 a kan tuhume-tuhume guda na fyaɗe, wanda rundunar ‘yan sandan ta ce ya saba wa sashe na 25 (a) na dokar cin zarafin jama’a ta jihar Ondo ta shekarar 2021.

Dan sanda mai shigar da ƙara, Sufeto Martins Olowofeso, ya shaida wa kotun cewa an kama wanda ake ƙara ne a ranar 18 ga watan Yuni, 2024 bayan rahoton da aka kai ga sashin yaki da garkuwa da mutane na ’yan sanda a Alagbaka, cewa ya yi wa ’yarsa fyaɗe.

Daga bisani an tsare wanda ake tuhuma don ci gaba da bincike.

A cewar Mista Olowofeso, wanda ake zargin tare da matarsa ​​sun gudu daga gidansu bayan aikata laifin inda suka je Jihar Osun suka samo rahoton likita na ƙarya, da ke nuna babu wani abu da ya samu yarinyar.

Ya kuma shaida wa kotun cewa jami’in bincike na ’yan sanda ya sake yin wani gwaji a Akure, wanda ya nuna cewa an zakke wa yarinyar, kuma ta kwashe kwanaki uku tana zubar da jini.

A cewar Olowofeso, wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake zargin sa da shi a lokacin da jami’in da ke binciken ya yi amsa tambayoyi.

KU KUMA KARANTA: An ɗaure ɗan shekara 17 shekaru 14 a kurkuku saboda fyaɗe

Olowofeso ya buƙaci kotun da ta ci gaba da tsare wanda ake ƙara a gidan gyaran hali na Olokuta har zuwa lokacin da za ta samu da shawara daga sashen shigar da kara na gwamnati (DPP).

Lauyan wanda ake ƙara, G.O Omoedu, ya shaida wa kotun cewa an kai wa wanda yake karewa sammaci ƙurarren lokaci kuma zai buƙaci lokaci domin ya mayar da martani kan batun shari’a.

Ya buƙaci kotun da ta dage ci gaba da shari’ar don ba shi damar amsa buƙatar ci gaba da sauraren ƙarar.

Majistare B.A. Alipohul ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake ƙara a hannun ’yan sanda sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 4 ga watan Yulin 2024.

Continue Reading

Laifi

’Yan bindiga sun sace Hakimi da manoma 2 a Kaduna

Published

on

’Yan bindiga sun sace Hakimi da manoma 2 a Kaduna

’Yan bindiga sun sace Hakimi da manoma 2 a Kaduna

’Yan bindiga sun yi garkuwa da Hakimin Tunburku, Malam Ashiru Sherehu da ke Ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewar, maharan sun yi awon gaba da Sherehu a kan hanyarsa ta dawowa daga gona a ranar Asabar.

’Yan bindiga sun addabi yankin da ke gundumar Fatika a ‘yan kwanakin nan da hare-hare.

A cewar wani mazaunin yankin, Ahmadu, manoma ba sa iya zuwa gonakinsu da ke da nisan kilomita kaɗan daga garin saboda tsoron kada a kashe su ko kuma a sace su.

Wani basaraken gargajiya a yankin kuma Sarkin Fadan Galadimawa, Husseini Umar, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an yi garkuwa da hakimin ƙauyen da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Asabar.

KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai da dama a jihar Delta

“Yana dawowa daga gonarsa da ke Tunburku sai ‘yan bindigar suka tare shi suka tafi da shi. Har yanzu ba mu ji daga gare su ba; kuma ba su tuntuɓe mu ba,” in ji shi.

A cewar Hussaini, an kuma sace wasu manoma biyu a yankin Sabon Layi da ke gundumar Kidandan a lokacin da suke aiki a gonakinsu a ranar Lahadi da rana.

Ya bayyana cewar mutanen ƙauyen da lamarin ya faru a gabansu sun kasa yin komai saboda ’yan bindigar na ɗauke da makamai.

Umar, ya koka kan yadda ’yan bindiga ke yi wa manoma ɗauki ɗai-ɗai a yankin.

Amma, ya yaba da ƙoƙarin sojojin da aka tura yankin, sai dai ya roƙi gwamnati da ta aike da ƙarin jami’an tsaro masu yawa saboda yadda rashin tsaro ke ƙara ta’azzara a yankin.

Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ba ta ce komai kan faruwar lamarin ba.

Jin ta bakin kakakin rundunar, ASP Mansir Hassan, ya ci tura domin ba ya amsa ƙiran waya.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like