Connect with us

Laifi

An kama ƙasurguman masu garkuwa da mutane 33 a Nasarawa

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta ce ta kama wasu ƙasurguman masu garkuwa da mutane 33 da suka addabi sassa daban-daban a Jihar Nasarawa.

Cikin wadanda aka kama har da waɗanda suka yi garkuwa da wasu ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Lafiya da ke Unguwar Gandu a yankin Mararaba a jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Shehu Umar Nadada a yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar rundunar a ranar Alhamis a Lafiya ya bayyana cewa, an kama dukkan waɗanda ake zargin ne a maɓoyarsu daban-daban.

Ya ce, “waɗanda aka kama su 13 ne da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, 11 da ake zargin ’yan fashi da makami ne, ɗaya da ake zargin ɓarawon shanu ne da kuma waɗanda ake zargi da aikata fyaɗe biyar, ciki har da wasu mutane biyu da ake zargin su zamba.

A cewarsa, “A ranar 4 ga Afrilu 2024, an samu labarin cewa an yi garkuwa da mutane huɗu a Rukubi, kuma an tura sashin yaƙi da garkuwa da mutane na rundunar don bin diddigin waɗanda ake zargin tare da kuɓutar da waɗanda abin ya shafa.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama wani mutum bisa zargin kashe abokinsa da sace motarsa a Kano

“Bayan nasarar da aka samu tare da ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su, yayin da aka kai su garin Rukubi, waɗanda abin ya shafa sun ga ɗaya daga cikin waɗanda suka yi garkuwa da su mai suna Shagari Ibrahim na garin Kadarko, Ƙaramar Hukumar Keana, inda nan take aka kama shi.

“Da aka yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifinsa ga Hukumar da aikata laifin.

“Sannan ya ƙara da ɗaukar alhakin sace wasu ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Lafiya a Otal ɗin Confidence da ke kan titin Makurdi, zuwa Lafiya.

“Daga nan ya amsa cewa ya gudanar da ayyukan garkuwa da mutane a Rukubi da Gandu da Kadarko da Agyaragu.

“A ranar 14 ga Afrilu 2024 da misalin ƙarfe 3:00 na rana, bisa samun sahihan bayanai, jami’an ‘yan sanda da ke ofishin ‘B’ Division, Lafiya sun kama wani Umar Idris mai unguwar Rukubi a Ƙaramar Hukumar Doma bisa zargin satar shanu inda aka samu kuɗi miliyan ɗaya da ɗari uku da dubu talatin a hannunsa.

“Wanda ake zargin ya amsa laifin satar shanu yana mai cewa ita ce babbar hanyarsa ta samun kuɗi; an kama shi ne a gidan karuwai a lokacin da yake jin daɗin aikata laifin.”

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Laifi

Ƴan sanda a jihar Yobe sun kama wata mata da kashe mijinta da wuƙa

Published

on

Ƴan sanda a jihar Yobe sun kama wata mata da kashe mijinta da wuƙa

Ƴan sanda a jihar Yobe sun kama wata mata da kashe mijinta da wuƙa

Ana zargin wata matar aure, Zainab Isa, mai kimanin shekara 22 ta kashe mijinta Ibrahim Yahaya Mai kimanin shekara 25 mazaunin unguwar Abbati cikin garin Damaturu a Jihar Yobe.

Lamarin ya faru ne sakamakon taƙaddamar da ta auku tsakanin ma’uaratan ranar Talata wadda ya kai ga ta soka wa mijinta nata wuƙa kuma nan take ya ce ga garinku nan.

Wata majiyar da ke unguwar ta Abbari ta bayyana cewar, ma’auratan sun daɗe suna takun saƙa a tsakaninsu, amma abinka da ajali taƙaddamar ƙarshen ita ce ta kai ga matar ta aika da mijin nata lahira.

Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta bakin kakakinta, DSP Dungus Abdulkarim ta tabbatar da faruwar wannan mummunan lamari.

Wakilinmu ya ruwaito cewa DSP Dungus ya yi wa manema labarai ƙarin haske kan faruwar lamarin da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar 26 ga Yuni a hedikwatar ’yan sanda ta C Division a da ke birnin Damaturu.

Kakakin ’yan sandan ya ce sun samu ƙorafin faruwar lamarin daga wani maƙwabcin ma’auratan da ke unguwar ta Abbari.

Ya ce makwabcin ya bayyana musu cewar ma’auratan sun yi musayar yawu a tsakaninsu, lamarin da ya rikiɗe zuwa rikici.

KU KUMA KARANTA: An kama wani matashi ɗan shekara 25 da laifin kashe mahaifinsa da wuƙa a Kano (Bidiyo)

Bayanai sun ce ana tsakar jayayyar ce sai matar ta yi amfani da wuƙa ta daɓa wa mijin a ƙirji, kuma daga baya ya mutu sakamakon mummunan rauni da ya samu kafin tawagar ‘yan sanda ta ƙaraso gidan.

DSP Dungus tuni aka miƙa matar sashen binciken manyan laifuffuka domin ɗaukar matakan da suka dace gabanin gurfanar da uta a gaban kuliya.

A bayanin da ta yi wa ’yan sandan, matar ta ce ba ta yi niyyar kashe mijinta ba, sai dai ta daɓa masa wuƙa ne domin ta kare kanta sakamakon dukan tsiya yake mata a lokacin faruwar lamarin duk da cewa ba ta gama samun sauƙi daga tiyatar da aka yi mata kwanan nan a dalilin haihuwar da ta yi ƙasa da wata guda.

Ta ci gaba da cewa “mun sha fuskantar matsaloli da tashin hankali a rayuwar aurenmu.

“Kusan kullum sai mun yi rikici da shi [mijin nawa] musamman idan na nemi kuɗin cefanen abinci tun lokacin aurenmu har bayan haihuwar ɗanmu na farko da na biyu.”

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Garba Ahmed, ya buƙaci ma’aurata da su riƙa miƙa rahoton  duk wani nau’i na cin zarafinsu da suke fuskanta a tsakaninsu ga mahukunta mafi kusa.

Kwamishinan ya ce wannan ita kaɗai ce hanyar da za a samu mafita mai ɗorewa ko kuma a kai ƙara kotu ko kuma miƙa wa ’yan uwa mafi kusa ƙorafi domin a yi musu sulhu maimakon ɗaukar mummunan mataki irin haka.

Ya kuma yi ƙira da umartan ’yan uwa da su riƙa  magance matsalolin da suka shafi zamantakewar aure kan lokaci don hana ta’azzara daga ƙananan rikice-rikice zuwa manya kamar kisan kai.

Continue Reading

'Yansanda

‘Yan sanda sun kama kawali na ’yan bindiga

Published

on

'Yan sanda sun kama kawali na ’yan bindiga

‘Yan sanda sun kama kawali na ’yan bindiga

Daga Muhammad Kukuri 

Wani wanda yake kai wa ’yan bindiga karuwai domin yin lalata da su ya shiga hannun jami’an tsaro.

’Yan sanda sun bayyana cewa kawalin ya kuma ƙware wajen yin safarar makamai ga ƙungiyar jagoran ’yan bindiga mai suna Arɗo, wanda ake nema ruwa a jallo a yankin Kagarko da ke Jihar Kaduna.

An kuma gano cewa mutumin wanda yake harkar hada-hadar tura kuɗi ta PoS, shi ke kai wa iyalan ’yan bindiga kuɗaɗe a yankin na Kagarko.

Dubun kawalin ta cika ne a yayin wani samamen haɗin gwiwa da ’yan sanda suka gudanar a yankin.

Kwamishinan ’Yan Sandan Birnin Tarayya, ya sanar ranar Talata cewa wanda ake zargin ya shaida musu cewa shi ke tsara yadda ake kai wa ’yan bindiga karuwai da miyagun ƙwayoyi da ma’aikatan lafiya a duk lokacin da suke buƙata.

KU KUMA KARANTA: Ƴan sanda a Kano sun kai mutanen da ake zargi da sayar da dala ba bisa ƙa’ida ba kotu

“Ya kuma amsa cewa yana yin dakon kuɗi tare da rabawa ga iyalan ’yan bindiga.

“A cewarsa, kuɗaɗen da ya raba wa iyalan ’yan bindiga sun haura Naira miliyan ashirin,” in ji kwamishinan ’yan sandan.

Igwe ya ce wanda ake zargin ya tabbatar musu cewa ’yan bindigar da ke ƙarƙashin Ardo sun kai 15 kowannensu da bindiga ƙirar AK-47.

Continue Reading

'Yansanda

’Yan sanda sun kama wani mai shekaru 45 ɗauke da ƙoƙon kai a jihar Ogun

Published

on

’Yan sanda sun kama wani mai shekaru 45 ɗauke ƙoƙon kai a jihar Ogun

’Yan sanda sun kama wani mai shekaru 45 ɗauke da ƙoƙon kai a jihar Ogun

Daga Muhammad Kukuri

’Yan sanda sun kama wani mai shekaru 45 da ake zargin matsafi ne ɗauke ƙoƙon kan mutum a garin Abeoluta na Jihar Ogun

Ana zargin mutumin yana shirin yin tsafi da ƙoƙon kan ne a lokacin da ’yan sanda suka kama shi.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sandan Kenya 400 sun tafi Haiti don aikin wanzar da zaman lafiya

Kakakin ’yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ta ce jami’an rundunar sun kama wanda ake zargin ne bayan da ya haka wani kabari ya sare kan gawar da ke ciki domin yin tsafi a garin Abeokua.

Odutola ta sanar a ranar Talata cewa rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like