Daga Ibraheem El-Tafseer
‘Yan tawayen Houthi sun kai wa tankar man Birtaniya da ke wucewa ta tekun Maliya hari da makami mai linzami.
Rahotonnin sun ce akwai ma’aikata 22 a cikin jirgin.
Jim kaɗan bayan harin ne, wani jirgin sojin ruwan Indiya da aka girke a yankin don yaƙar ‘yan tawayen ya fara mayar da martani.
Cikin wani saƙo da jami’an jirgin sojin ruwan suka wallafa a shafin sada zumunta, sun ce jirgin ya harba na’urar da ke kakkaɓo makami mai linzami don daƙile harin ‘yan tawayen kan tankar man Birtaniyar, bayan da ya samu ƙiran taimako.
KU KUMA KARANTA: Jirgi ya yi saukar gaggawa bayan fasinja ya gartsa wa ma’aikaciya cizo
A baya-bayan nan dai ana samun ƙaruwar hare-hare kan jiragen ruwa a tekun Maliya, bayan da ‘yan tawayen Houthi suka ce za su riƙa kai hari kan duk wani jirgin ruwan Isra’ila ko wanda ke kan hanyar zuwa Isra’ila, domin nuna adawarsu da hare-haren da Isra’ila ke kai wa Falasɗinawa Gaza.