An kai sabbin hare-hare a kusa da Chibok, an kashe mutum 15

0
145

Wasu mayaƙan ƙungiyoyin da ke iƙirarin jihadi sun kashe aƙalla mutum 15 a hare-haren da suka kai a ƙauyuka biyu da ke kusa da Chibok da ke jihar Borno a arewacin Najeriya, a cewar mazauna yankin ranar Laraba.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wasu mazauna yankin suna cewa ‘yan bindiga a cikin motocin a-kori-kura da kan babura ɗauke da manyan bindigogi sun kai hari a ƙauyukan Gatamarwa da Tsiha ranar Litinin, inda suka kashe mutanen tare da ƙona gidajensu bayan sun sace kayan abinci.

“Mutum 15 ne suka mutu sakamakon hare-haren da aka kai a ƙauyukan biyu,” in ji Manasseh Allen, shugaban ƙungiyar Ci-gaban Yankin Chibok (CADA), a hira da AFP.

Babu cikakken bayani game da ko mayaƙan Boko Haram ne suka kai harin ko kuma abokan adawarsu na ƙungiyar ISWAP.

KU KUMA KARANTA: An sake ceto ƴan matan Chibok biyu a Jihar Borno

Maharan, sanye da kakin sojoji, sun shiga kauyen Gatamarwa, inda suka buɗe wuta kan mutane, ciki har da masu zaman makoki jim kadan bayan sun dawo daga wata jana’iza, a cewar Allen.

“Maharan sun kashe mutum 12 a ƙauyen Gatamarwa sannan suka kashe mutum uku a Tsiha,” in ji shi.

Wasu mutum biyu sun tabbatar da wannan bayani na Allen.

“Bayan kase-kashen, maharan sun kwashi kayan abinci sannan suka cinna wuta a kayukan biyu,” in ji Ayuba Alamson, wani dattijo a Chibok, yana mai tabbatar da adadin mutanen da aka kashe.

Kazalika maharan sun sace wata budurwa a Tsiha, in ji wani mazaunin kauyen mai suna Samson Bulus.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno Nahum Daso ya tabbatar da kai hare-haren, amma ya ƙi yin ƙarin bayani game da adadin mutanen da aka kashe.

Chibok ya ja hankalin duniya a 2014 lokacin da mayaƙan Boko Haram suka sace mata ‘yan makarantar-kwana fiye da 200.

Leave a Reply