No menu items!

Sample Page Title

Date:

Mahara ɗauke da muggan makamai sun kai hari kan hedikwatar ’yan sanda da ke Jihar Adamawa.

Rugugin luguden harbe-harben maharan a cikin dare ya jefa mazauna garin Jimeta da ke ƙaramar hukumar Yola ta Arewa a jihar cikin tashin hankali.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya tabbatar wa Aminiya cewa hedikwatar rundunar ce aka kai wa hari, kuma ba a kai ga gano maharan ko manufarsu ba.

Sai dai ya bayyana cewa jami’an rundunar sun yi nasarar fatattakar maharan, bayan musayar wuta ta kusan minti 30 da misalin ƙarfe 11 na daren Talata.

Wasu majiyoyi dai sun yi zargin maharan sojoji ne suka kai harin ɗaukar fansa kan hedikwatar rundunar kan kisan wani hafsan soja da wani ɗan sanda ya yi.

Kawo yanzu dai ana bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...