An kafa wata rundunar tsaro ta musamman a jihar Filato

0
150

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ƙaddamar da wata runduna ta musamman da za ta yi yaƙi da ɓata-gari da ke kashe-kashen rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar Filato.

Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun wanda ya kai ziyarar gani da ido kan asarar rayuka da dama a wasu ƙananan hukumomin jihar Filato, ya ce rundunar ta musamman da gwamnatin tarayya ta amince da kaddamarwa a jihohi goma na Najeriya, zata fara aiki ne nan take a jihar Filato.

Tuni da mataimakin Sufeta Janar na shiya ta huɗu, Ebong Eyibio ya ƙaddamar da jami’an runduna ta musamman zuwa yankunan da ke fuskantar matsalolin tsaron.

A ci gaba da neman mafita kan batun ƙalubalen tsaron, Sanata mai wakiltar tsakiyar Filato, Diket Plang ya gabatar da wassu batutuwa a gaban majalisar dattawan, da ya ce za su taimaka wajen kawo dawwamammen zaman lafiya a jihar.

Sanata Diket Plang ya koka kan yadda maharan su ɗari huɗu suka ratsa wurare suka mamaye ƙauyuka fiye da ishirin ba tare da wani ya gansu ba.

KU KUMA KARANTA: Kashim Shettima ya kai ziyara jihar Filato don jajanta waɗanda harin ta’addancin ranar Kirsimeti ya shafa

Ya kuma koka kan yadda wasu ke mamaye gonaki da gidajen waɗanda suka yi gudun hijira, tare da yin ƙira ga gwamnatin tarayya da ta samar da jami’an tsaro na dindindin a yankunan.

A cewar Dah Mai’anguwa, Jamok Mafwalal Machambe daga gundumar Butura a karamar hukumar Bokkos, sun yi na’am da zuwan jam’an tsaron, ya kuma buƙaci jama’a su basu goyon baya don samar da tsaro.

Sakataren ƙungiyar miyetti Allah a ƙaramar hukumar Barkin Ladi, Abubakar Gambo yace suna buƙatar jami’an tsaron su yi adalci.

A ƙoƙarin masu ruwa da tsakin na lalubo hanyoyin samun mafita kan lamarin tsaron, tambayoyin da ke bakunan al’ummar Filato sune, su wanene ke aikata kashe-kashen, daga ina suke fitowa? me suke buƙata? wanene ke ba su makamai da sauran kayan aiki? yaushe ne za su kammala aikin nasu? Lokaci zai bayyana abin da ke faruwa.

Leave a Reply