An jinjina wa Kashim Tumsa bisa ga samar da fitulun sola 400 a Bursari (hotuna)

0
258
An jinjina wa Kashim Tumsa bisa ga samar da fitulun sola 400 a Bursari (hotuna da bidiyo)

An jinjina wa Kashim Tumsa bisa ga samar da fitulun sola 400 a Bursari (hotuna) 

Jama’a suna jinjina wa Kashim Tumsah da wasu abokan arziƙi bisa ga samar da fitilu masu inganci kuma masu amfani da hasken rana a sassa sama da dari huɗu (400) a ƙaramar hukumar Bursari.

Biyo bayan ƙarfafa masa guiwa da shawarwarin haziƙin ɗan Majalisar Bursari Hon. Zanna Baba Gana.


Wannan Fitilu masu amfani da hasken rana an kafasu a tsangayoyi, Islamiyoyi, kasuwanni da sauran wurare a fadin ƙaramar hukumar Bursari ta jihar Yobe.

KU KUMA KARANTA:Gidauniyar MJ Alƙali ta raba wa marayu 100 kayan Sallah a Yobe (Hotuna)

Sunayen ƙauyukan da suka amfana da wutar lantarkin sun haɗa da;

1. Dapchi
2. Turbangida
3. Matti
4. Umarari
5. Goniri
6. Mangari
7. Bayamari
8. Damaya
9. Ajiri
10. Garin Aduwa
11. Aji Dawari
12. Kaliyari
13. Harunari
14. Kakanderi
15. Juluri
16. Gamsawa
17. Kankare
18. Sabongari
19. Jawa
20. Garun Dole
21. Masaba
22. Dumburi
23. Kabaya
24. Sunowa
25. Mari
26. Koromari Kura
27. Baya Malumbe
28. Korsori
29. Abbari
30. Kurnawa
31. Damnawa

Allah Ya sakawa duk wanda yake da hannu wajen kawo waɗannan abin ci gaba da muka samu a Bursari.

Leave a Reply