An harbi masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Kaduna

0
254

’Yan sanda a jihar Kaduna sun tarwatsa ’yan ƙungiyar ’yan uwa Musulmi ta Najeriya (IMN) ta mabiya Shi’a da ke zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa.

Masu zanga-zangar dai na goyon bayan Falasɗinawan ne waɗanda yanzu haka ƙasar Isra’ila ke yi wa luguden wuta a Zirin Gaza.

’Yan Shi’ar dai sun fara zanga-zangar ne dai daga sakatariyar Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) sannan suka bi titin Muhammadu Buhari, zuwa ofishin Hukumar Kare Hakkin Ɗan Adam (NHRC), inda suka miƙa takardar kokensu.

Sai dai ’yan mintuna bayan fara zanga-zangar, sai ’yan sanda suka fesa musu barkonon tsohuwa sannan suka yi harbi a sama domin tarwatsa su.

KU KUMA KARANTA: Lauyoyin Falasɗinawa sun shigar da Isra’ila ƙara a kotun ICC

Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce sakamakon harbin, mutum biyu sun rasa ransu.

Aliyu Umar Tirmizi, wanda ya yi magana a madadin masu zanga-zangar, ya ce, “Tsawon shekara 75 ke nan Isra’ila na aiwatar da kisan kiyashi da kisan kare-dangi da wariyar launin fata a kan fararen hular da ba su ji ba, ba su gani ba, cikinsu har da maza, mata da ma ƙananan yara.

“Sun kashe dubban ƙananan yara da tsofaffi sannan sun lalata wuraren ibada da na ibadar mutanen da ba ruwansu.

“Waɗannan Yahudawan na Isra’ila sun keta alfarmar masallacin birnin Kudus, sun hana mutane zuwa ciki domin yin ibada,” in ji Timizi.

Tun bayan harin rokoki da ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa ta ƙaddamar a kan Isra’ila, ƙasar ta ke kai hare-haren ramuwar gayya, inda zuwa yanzu ta kashe sama da mutum 12,000 a Zirin Gaza.

Leave a Reply