An harbe mutane 4 a rikicin da ya ɓarke tsakanin jama’a da jami’an tsaro kan rusau a Kano

0
22
An harbe mutane 4 a rikicin da ya ɓarke tsakanin jama'a da jami’an tsaro kan rusau a Kano

An harbe mutane 4 a rikicin da ya ɓarke tsakanin jama’a da jami’an tsaro kan rusau a Kano

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Ana fargabar harbe mutane hudu 4 sun mutu a Rimin Zakara a karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano, bayan rikici ya ɓarke tsakanin mazauna yankin jami’an tsaro kan rushe wasu gine-gine.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro ne su ka harbi mutane shida 6 a wajen, inda hudu suka rasu sauran biyu kuma su ka jikkata bayan da mazauna yankin suka mayar da martani kan rushe musu gidaje.

Majiyoyi sun ce gine-ginen da aka rushe kimanin 40, mafi yawansu gidaje ne da ba a kammala ba, an riga an yi wa alamar dakatawa da ginin daga Hukumar Kula da Tsare-tsaren Birane ta KNUPDA.

Rahotanni sun ce filayen da ake rikici akai mallakin Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ne.

KU KUMA KARANTA:Kotu ta haramtawa gwamnatin Kano rusau a Jihar

Wani mazaunin yankin da abin ya shafa, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa KNUPDA ta riga ta tantance cewa filayen sahihai ne.

Kokarin jin ta bakin KNUPDA ya ci tura, domin ba a samu shugaban ta ba, sai dai wata majiya a hukumar ta tabbatar da cewa ba su ne su ka yi rusau din ba.

Wani jami’i daga ma’aikatar filayen, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya tabbatar da cewa filayen mallakin Jami’ar BUK ne, kuma gwamnati za ta fitar da sanarwa nan ba da jimawa ba a kan lamarin.

Sai dai Kakakin Hukumar Tsaron Farar Hula na NSCDC, Ibrahim Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce matasa ne su ka kai musu hari har su ka jikkata jami’in ta .

A cewar sa, an kai jami’an tsaron ne don su kare ma’aikatan da su ke aikin rusau din, shi ne mazauna unguwar su ka far musu.

“Su ka raunata jami’an mu kuma su ka farfasa mans mota,”

Leave a Reply