No menu items!

Sample Page Title

Date:

An haifi jaririn da ya yi shekaru shekaru 30 a ciki, a ƙasar Amurka

Daga Jameel Lawan Yakasai

Wani jariri namiji da aka haifa a jihar Ohio da ke Amurka, ya zama “jariri mafi tsufa a duniya” bayan an haife shi daga ɗan ciki da aka daskare fiye da shekaru 30 da suka gabata.

Kafar yada labarai ta DCL Hausa ta rawaito cewa Jaririn mai suna Thaddeus Daniel Pierce an haife shi ne a ranar 26 ga Yuli ta hanyar dashen ciki na IVF da ma’auratan Lindsey da Tim Pierce daga birnin London, Ohio, suka yi ta hanyar ɗaukar ciki daga wata asibiti.

KU KUMA KARANTA: An ceto wani jariri da aka kashe mahaifiyarsa a wani mummunan farmaki ta sama a Gaza

Rahoton MIT Technology Review ya bayyana cewa an daskarar da ɗan cikin tun watan Mayun shekarar 1994.

Lindsey ta bayyana cewa mijinta, Tim mai shekaru 35, yana ƙaramin yaro ne lokacin da aka kirkiri ɗan cikin da yanzu ya zama ɗansu.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...