No menu items!

Sample Page Title

Date:

An haɗa Najeriya, Tunisiya, Tanzaniya da Uganda a gasar AFCON 2025

An haɗa tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya ‘Super Eagles’ da takwararta ta Tunisiya, sannan an hada Tanzaniya da Uganda a gasar cin kofin nahiyar Afirka mai zuwa da kasar Morocco zata karbi bakunci.

An shigar da tawagar Najeriyar ne a rukunin “C” yayin wani biki daya gudana a Morocco a jiya Litinin.

A karawar ta cikin rukuni da zata dauki hankula, Najeriya zata kece raini da tawagar Carthage Eagles ta kasar Tunisiya.

KU KUMA KARANTA:Gasar AFCON 2025: CAF za ta binciki halin da ‘yan Super Eagles suka fuskanta a filin jirgin Libya

Zakarun gasar a gida a 2004, Tunisiya ta doke Najeriya a wasan kusa dana karshe kafin tayi tafiyar ruwa da Morocco a wasan karshe. haka kuma tawagar kasar Tunisiya ta taba fidda Najeriya daga gasar afcon ta 2021 a Kamaru.

Najeriya ta taba samun galaba akan Tunisiya da ci 4-2 a kokarin kaiwa wasan karshe na AFCON ta 2000 inda ta hadu da kasar Kamaru.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...