An gurfanar da wasu kan zargin sanya wa yara wiwi a cikin fanke

Wasu mutum biyu na fuskantar tuhuma kan yunƙurin kisan kai a Afirka ta Kudu bayan da wasu yara kusan 90 suka kamu da rashin lafiya bayan cin fanke da aka sanya wa tabar wiwi.

Jami’ai sun ce yaran sun sayi fanken ne a wajen wani mutum a gefen titi a kan hanyarsu ta zuwa makarantar firamare ta Pulamadibogo, a arewa maso yammacin Pretoria.

An kai da dama daga cikinsu asibiti saboda tashin zuciya da ciwon ciki da kuma amai.

An zargi mutanen biyu masu shekaru 21 da kuma 19 da yunƙurin aikata kisa a ranar Juma’a.

Ma’aikatar ilimi ta lardin Gauteng ta ce malamai sun ƙira motar ɗaukar marasa lafiya bayan da suka lura cewa ɗalibansu sun fara nuna wasu halaye a cikin aji.

KU KUMA KARANTA: Wata matashiya a jihar Abiya, ta kashe mahaifiyarta ta hanyar sa mata guba a abinci

Ta ce lamarin ya haifar da damuwa matuƙa ga iyayen yaran.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta fitar, ta ce an garzaya da dukkan ɗaliban zuwa asibitoci da ke kusa, inda zuwa yanzu aka sallami kusan 87.

Ma’aikatar ta ce ‘yan mata uku ne kaɗai suka rage a asibiti, kuma suna ci gaba da samun kulawa yadda ya kamata.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *